Ladubban SoyayyaD- Rowa
219. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Babu alheri ga aboki marowaci[19]. 220. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Rowa tana kawo gaba da kiyayya[20]. 221. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Rowa tana kaskantar da mai yenta, kuma mai nisantarta yana daukaka[21]. E- Sakin Jiki
222. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Kada ka amincewa abokinka gaba daya, ka sani kayen nan na sakin jiki ba a iya mayar da hasararsa[22]. F- Cutarwa
223. Kanzul Ummal; daga Anas: Daga Manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan ya tsaya da dare yana karatu, sai ya yi sauti da murya kadan a cikin karatunsa, sai aka yi masa magana game da hakan, aka ce masa: me ya sa ba ka dada sautinka a karatu? sai ya ce: Ina kin in cutar da wani abokina da ahlin gidana[23]. G- Wulakanci
224. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ku kasance bayin Allah kuna ‘yan’uwa, musulmi dan’uwan muslumi ne, kada ya zalunce shi, kada ya tabar da shi, kuma kada ya wulakanta shi[24]. H- Wuce Gona Da Iri A Kauna
225. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ka so masoyanka da sauki haka nan, ta yiwu ya kasance makiyinka a wata rana haka nan, ka ki makiyinka da sauki haka nan, tayiwu ya kasance masoyinka wata rana haka nan[25]. 226. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: kada sonka ya kasance kallafa wa kai, kuma kada kin ka ya kasance a banza; ka so masoyinka da sauki haka nan, kuma ka ki makiyinka da sauki haka nan[26]. I- Sabo Saboda Aboki
227. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mumini ba ya zaluntar wanda yake ki, kuma ba ya daukar alhaki domin wanda yake so[27]. J- Yada Duk Wani Sirri
228. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ka ba wa abokinka dukkan soyayya, kada ba shi dukkan nutsuwa, ka ba shi dukkan taimako, kada ka ba shi dukkan asirai; (da haka ne) zaka ba wa hikima hakkinta, kuma ka yi wa abokinka abin da yake wajibi ne a kanka[28].
|