Ladubban SoyayyaE- Cudedeniya
210. Daga Imam Ridha (A.S): yayin da aka tambaye shi mene ne hankali: juriya kan bakin ciki, da kuma raha ga makiya, da kuma cudanyar abokai[10]. 6 / 2 Abin da bai kamata ba a zamantakewar ‘yan’uwa
A- Batar Da Kama
211. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: uku Allah ba ya kallon su ranar alkiyama kuma ba ya tsarkake su kuma suna da azaba mai radadi: mai jan wandonsa kasa saboda girman kai, da mai yabon kayan sayarwarsa da karya, da kuma mutumin da ya fuskance ka da so da kauna a zuciyarsa amma sai ya wuce ya kule (ya bace daga gani), zuciyarsa tana cike da algush[11]. 212. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: idan ilimi ya bayyana, aka tsare aiki, kuma aka hadu a harsuna, aka saba a zukata, aka yanke zumunci, to a nan ne “Allah ya la’ance su kuma ya kurumtar da su, kuma ya makantar da ganinsuâ€[12]. 213. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Da yawa mai kauna ya zama na karya ne[13]. B- Mummunan Zato
214. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Kada zato ya bata maka wani aboki da yakini ya gyara maka shi[14]. 215. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: Kada mummunan zato ya yawaita gareka; domin ba zai bar maka wani sulhu ba tsakaninka da wani masoyi[15]. C- Algush
216. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: algus din aboki, da yaudarar alkawura, suna daga ha’incin alkawari[16]. 217. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: kada ka yi wa mutane algush sai ka wanzu ba ka da wani aboki[17]. 218. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: kada wani mai girman kai ya yi tsammanin yabo kyakkyawa, haka nan kada mayaudari ya yi tsammanin samun yawan abokai[18].
|