Ladubban Soyayya



Ladubban Soyayya

6 / 1

Abin Da Ya Kamata A Cikin Zama Da ‘Yan’uwa

A- Sanin Siffofi

201. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: idan wani ya yi abota da wani to ya tambaye shi sunansa da sunan babansa da kuma waye shi; wannan ya fi sadar da soyayya[1].

B- Shelanta Soyayya

202. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: idan dayanku yana son wani to ya sanar da shi; domin cewa; shi ma (wancan) zai ji irin abin da yake ji gunsa[2]

203. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: idan dayanku yana son wani to ya sanar da shi, domin wannna ya fi wanzar da soyayya, kuma ya fi tabbatar da kauna[3].

204. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: idan ka so wani daga ‘yan’uwanka to ka sanar da shi hakan, hakika Ibrahim (A.S) ya ce; “Ubangiji ka nuna mini yadda kake raya matattu, ya ce; shin ba ka yi imani ba ne, sai ya ce; na yi imani, amma sai dai domin zuciyata ta samu nutsuwa ne”[4].

C-Kiyaye Dadaddiyar Soyayya

205. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: hakika Ubangiji madaukaki yana son lizimtuwa a kan dadaddiyar ‘yan’uwantaka, ku dawwama a kanta[5].

206. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafificin kowane abu shi ne; sabonsa, mafificin ‘yan’uwa mafi dadewarsu[6].

207. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Kaunar wuni sadar da zumunci ce, kuma kaunar wata kusanci ce, kaunar shekara sadar da zumunci ne madawwami, wanda ya yanke ta Allah zai yanke shi[7].

D- Sakin Fuska Yayin Haduwa

208. Daga Imam Muhammad Bakir (A.S): wani mutum ya zo wa Manzon Allah (S.A.W), sai ya ce: Ka yi mini wasiyya. Ya kasance daga abin da ya yi masa wasiyya ya ce masa: ka hadu da dan’uwanka da fuska sakakkiya[8].

209. Daga littafin Kafi daga ibn mahbub daga wasu daga sahabban Abu Abdullahi (A.S) ya ce masa: mene ne iyakacin kyakkyawar dabi’a? sai ya ce: ka tausasa masa, ka dadada masa magana, ka kuma hadu da dan’uwanka da sakakkiyar fuska mai kyau[9].



1 2 3 4 5 6 7 next