Masu Hana Soyayya



n- Hassada

136. Imam Ali (A.S) ya ce: Babu abota ga mai yawan hassada[20].

137. Imam Ali (A.S) ya ce: hassadar aboki tana daga ciwon abotaka[21].

o- Yaudara

138. Imam Ali (A.S) ya ce: Abotakar masoyi ba ta dawwama tare da yaudara[22].

p- Isgili

139. Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: kada mai girman kai ya yi kwadayin yabo kyakkyawa… kada kuma mai yin isgili ga mutane ya yi kwadayin soyayyar gaskiya[23].

k- Yin Zunubi

140. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Na rantse da wanda ran Muhammad take a hannunsa, babu wasu mutane biyu da suka yi soyayya sai aka raba tsakaninsu sai domin sakamkon wani zunubi da dayansu yake yi[24].

r- Bin Mai Jita-Jita

 141. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya bi mai jita-jita ya rasa aboki[25].

s- Muzantawa (kwankwasa)

142. Imam Ali (A.S) ya ce: yawan muzantawa yana kawo kiyayyar zukata, da kuma dimautar (nisantar) da abokai[26].

t- Barin alkawari

143. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda bai riki masoyansa ba, to hakika ya tozarta (rasa) abokai[27].

u- Rashin adalci

144. Imam Ali (A.S) ya ce: wanda aka rasa adalcinsa, to ba za a yi abota da shi ba[28].

b- Hana alheri

145. Imam Ali (A.S) ya ce: hanin alherinka, yana sanya abota da waninka[29].



back 1 2 3 4 5 6 7 next