Masu Hana Soyayya



g- Daure fuska (juyawa)

126. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: wanda ya daure fuska ga dan’uwansa, to ya haramta a sadar da shi, wanda kuwa ya bakanta masa, alfarmarsa ta saraya[10].

h- Yin Kwauro

127. Imam Ali (A.S) ya ce: Daduwar kwauro tana munana samartaka, kuma tana bata ‘yan’uwantaka[11].

i- Tsanantawa

128. Imam Ali (A.S) ya ce: Tsanantawa yana muzanta halaye, yana kuma dimautar (nisantar) da abokai[12].

j- Kosawa

129. Imam Ali (A.S) ya ce: kosawa da juna, yana bata ‘yan’uwantaka[13].

130. Imam Ali (A.S) ya ce: da kyar ne dubarar gaggautawa take samun nasara, kuma da kyar ne abotakar mai kosarwa (mai dandano; wato yau yana tare da wannan gobe kuma yana tare da wani) take dawwama[14].

131. Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Kada ka yi shawara da wawa, kuma kada ka nemi taimako da makaryaci, kada ka aminta da abokantakar mai kosarwa; hakika… mai kosarwa matukar ka aminta da shi sai ya tozarta ka, kuma duk yadda ka sadar da shi sai ya yanke ka[15].

k- Girman Kai

132. Imam Ali (A.S) ya ce: mai girman kai ba shi da aboki[16].

133. Imam Ali (A.S) ya ce: Wanda ya daga kansa a kan ‘yan’uwansa, to babu wani mutum da zai rage gunsa[17].

l- jafa’i

134. Kada ka nemi ‘yan’uwantaka gun ma’abota jafa’i, ka neme ta gurin masu kiyayewa da cika alkawari da rikon amana[18].

m- Mugun Kulli

135. Imam Ali (A.S) ya ce: babu abota ga mai mummunan kulli (mugun kuduri) [19].



back 1 2 3 4 5 6 7 next