Zabar Masoyi (Aboki)



193. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin ‘yan’uwanka shi ne wanda ya fi taimakawarsu a kan alheri, kuma mafi aikatawarsu ga kyakkyawa, kuma mafi tausasawarsu ga aboki[49].

194. Daga Imam Hasan askari (A.S): mafi alherin ‘yan’uwanka shi ne wanda ya mance zunubinka (laifinka), ya tuna kyawawanka[50].

5 / 9

Mafi Gaskiyar ‘Yan’uwa

195. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: aboki ba ya kasancewa aboki har sai ya kiyaye dan’uwansa a abubuwa uku: a cikin wahalarsa, da boyuwarsa, da mutuwarsa[51].

196. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: aboki mai yawan gaskiya shi ne wanda ya yi maka nasiha a aibinka, kuma ya kiyaye ka a cikin fakuwarka, kuma ya zabe ka a kan kansa[52].

197. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: aboki shi ne; wanda ya kasance mai hani daga zalunci da gaba, mai taimako a kan kyakkyawa da kyautatawa[53].

198. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: hakika dan’uwanka bisa gaskiya shi ne; wanda ya yafe kuskurenka, kuma ya toshe aibinka, ya karbi uzurinka, ya suturta al’aurarka, ya kawar da tsoronka, kuma ya tabbatar da burinka[54].

199. Daga Littafin Kanzul fawa’id: an ruwaito Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) cewa: ya kasance saudayawa yana maimaita wadannan baitoci biyu;

Dan’uwanka shi ne wanda, da ka nufo shi da takobi zararre

Domin ka sare shi, da bai yaudare ka a kauna ba



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next