Zabar Masoyi (Aboki)Mafi alherin ‘yan’uwa
183. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mafi alherin cikin ‘yan’uwanka shi ne wanda ya taimaka maka a kan bin Allah, kuma ya hana ka sabonsa, kuma ya ya umarce ka da abin da yake yardarsa (Allah ) [39]. 184. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin cikin ‘yan’uwa shi ne wanda sonsa ya kasance saboda Allah ne[40]. 185. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin cikin ‘yan’uwa shi ne; mafi karancinsu aiwatarwa cikin nasiha[41]. 186. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin cikin ‘yan’uwa shi ne; mafi nasiharsu, mafi sharrinsu kuwa shi ne; mafi yaudararsu[42]. 187. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin cikin ‘yan’uwa shi ne wanda idan ka rasa shi to ba ka son wanzuwa bayansa kuma [43]. 188. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin cikin ‘yan’uwa shi ne wanda bai kasance mai neman nisantar ‘yan’uwansa ba[44]. 188. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin ‘yan’uwanka shi ne wanda ya nuna maka shiriya, kuma ya tufatar da kai takawa, kuma ya hana ka bin son rai[45]. 190. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin ‘yan’uwanka shi ne wanda ya yawaita fusata ka saboda (fadar) gaskiyarsa[46]. 191. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin ‘yan’uwanka shi ne wanda ya taimaka maka, mafi alheri daga gareshi kuwa shi ne; wanda ya isar maka, kuma idan ya bukace ka sai ya yi maka afuwa (rangwame; wato ba ya dora maka nauyi)[47]. 192. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi alherin ‘yan’uwanka shi ne wanda ya kira ka zuwa ga gaskiyar zance da gaskiyar zancensa, kuma ya soyar da kai zuwa ga mafi kyawun ayyuka da kyawawan ayyukansa[48].
|