Zabar Masoyi (Aboki)175. Lukman (A.S) yana gaya wa dansa: wanda ya yi abota da mai munin hali ba ya kubuta[31]. 5 / 7 Mafi Munin (Sharrin) ‘Yan’uwa
176. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwa shi ne wanda aka dora wa kai nauyi saboda shi[32]. 177. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwa shi ne mai sadarwa (makalewa) lokacin yalawa, mai rabuwa (gujewa) lokacin bala’i[33]. 178. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka shi ne; mai yin algush, mai yaudara[34]. 178. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka shi ne; wanda ya yardar da kai da barna[35]. 180. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka shi ne; wanda ya bukatar da kai zuwa ga cakuduwa (fadawa laifi), kuma ya tura ka zuwa ga bayar da uzuri[36]. 181. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka shi ne; wanda ya jinkirtar da kai ga barin alheri, kuma ya jinkirtar da kai tare da shi (ya sanya ka ci baya)[37]. 182. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: mafi munin (sharrin) ‘yan’uwanka kuma mafi algush dinsu, shi ne; wanda ya ya yaudare ka da magaggauciya (duniya), ya shagaltar da kai daga majinkirciya (lahira)[38]. 5 / 8
|