Zabar Masoyi (Aboki)157. Imam Muhammad Jawad (A.S) ya ce: wanda ya karkata zuwa ga nutsuwa kafin jarrabawa, to ya kai kansa ga halaka, kuma da karshe mai wahalarwa[9]. 5 / 3 Abin Da Ake Jarraba Abokai Da Shi
158. Imam Ali (A.S) ya ce: yayin da karfi ya kawu (kare) a nan ne ake gane masoyi da makiyi[10]. 158. Imam Ali (A.S) ya ce: a cikin tsanani ake jarraba aboki[11]. 160. Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: ba ka siffanta mutum a matsayin aboki – siffantawa ta sani- har sai ka jarraba shi da abubuwa uku: Ka fusata shi sai ka ga fushinsa yana fitar da shi daga gaskiya zuwa barna (karya), da kuma gun dinare da dirhami, da kuma tafiya tare da shi[12]. 161. Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: wanda ya yi fushi da kai sau uku, bai fadi mummuna a kanka ba, to ka rike shi masoyi gareka[13]. 162. Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Idan kana da aboki sai ya samu wani matsayi, sai ka gan shi yana zama da kai kamar yadda yake tare da kai kafin ya samu wannan matsayin da yake kansa, to ba mumman aboki ba ne[14]. 163. Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: ana jarraba aboki da dabi’u uku, idan ya kasance ya yi juriya tare da kai a cikinta to shi aboki ne nakwarai, idan kuwa ba haka ba, to shi abokin lokacin yalwa neb a na lokacin tsanani ba: ka nemi dukiya wurinsa, ko ka amintar da shi kan wata dukiya, ko ka nemi tarayya da shi a cikin wani abin wahala[15]. 5 / 4 Karancin Aboki Mai Gaskiya
164. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mafi karancin abin da ake samu a karshen zamani shi ne dan’uwan da ake aminta da shi, ko kuma dirhami na halal[16].
|