Kiyayya Don AllahKiyayya
1 / 2 Hattara Da Kiyayya
27. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ku sani a cikin gaba da juna da akwai mai askewa, ba ina nufin mai aske gashi ba, sai dai ita mai aske addini ce[1]. 28. Daga gareshi (S.A.W) ya ce: kada ku yanke juna, kada ku bayar da baya gajuna, kada ku yi kiyayya, kada ku yi hassara, ku kasance ‘yan’uwa[2]. 29. Imam Ali (A.S) ya ce: duniya ta yi kunci ga masu kiyayya da juna[3]. 2 / 2 Hanin Yankewa Juna
30.Imam Ali (A.S) ya ce: kada ka yanke alakar dan’uwanka bisa kokwanto, kuma kada ka yanke alakarsa babu wani laifi[4]. 31. Daga gareshi (A.S) ya ce: a wata wasika zuwa ga dansa Imam Hasan (A.S): ka dora wa kanka sadar da zumuncin dan’uwanka yayin da ya yanke zumuncinka, kuma haka nan ma yayin da ya kaurace maka, sai ka dora wa kanka a kan tausasawa da kusantowa, idan kuma ya yi mako sai ka ba shi, idan kuwa ya yi nisa sai ka yo kusa, idan kuwa ya tsananta sai ka tausasa, idan kuwa ya yi laifi sai ka bayar da uzuri, kai ka ce kai bawa ne gareshi, kamar shi kuma mai ni’imtawa ne gareka. Na hana ka sanya wani abu ba a mahallinsa ba, ko kuma ka aikata wani abu ba ga ahlinsa ba[5]. 32. Daga gareshi (A.S) ya ce: idan kana son ka yanke wa dan’uwanka to ka bar masa wata rara daga kanka da idan ya so komowa zuwa gareka wata rana to zai iya[6]. 33. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Iblis ba ya gushewa yana mai farin ciki matukar musulmai biyu suka kaurace wa juna, idan suka hadu (suka shirya) sai gwiwowinsa su yi makyarkyata, gabbansa su sassauta, ya yi ihu: wayyo kaiconsa, na abin da ya samu na tabewa[7]. 34. Daga gareshi (A.S) ya ce: wani mutum mai suna Hammam ya tashi wata rana –ya kasance bawa ne mai yawan ibada da kokari- wajen Imam Ali (A.S) lokacin yana huduba, sai ya ce: ya amirul muminin, siffanta mini siffar mumini kamar inaganinsa, sai Imam (A.S) ya ce: …ba ya kauracewa dan’uwansa, ba ya gibarsa, ba ya yi masa makirci[8].
|