Asasin KiyayyaAsasin Kiyayya
Hujjatul Islam Muhammad Raishahari
Hafiz Muhammad Sa’id Magana Game Da Alamomin Soyayya Saboda Allah
Mun riga mun tabbatar a kashi na farko na wannan littafin cewa musulnci addinin soyayya ne, kuma al’ummar da msulunci yake son kafawa ita ce al’ummar da ta tsayu a kan soyayya, kuma mun yi bayani a kashi na biyu cewa; soyayyar Allah ita ce mafi muhimmancin (sinadirin) abin da aka taskace na ginin daidaikun mutane da kuma al’umma da kuma kamalar duniya da lahira ta mutum. Mafi muhimmancin abu da za a iya fitarwa a cikin duba ga ayoyi da hadisai da suka zo a kashi na uku su ne cewa soyayya saboda Allah ita ce kawai tafarki guda daya don kai wa ga marhalar samun al’ummar da take abar koyi ce wajan tsayuwa a kan soyayya, kuma babu wata hanya watanta wacce za a iya samun ganin bayan kiyayya da fasadi da cizge su daga doron kasa, da kuma kai al’ummar dan’Adam zuwa ga rayuwar da ake burin samunta. Asasin Kiyayya Da Gaba
Da mun duba dukkan mabubbugan fasadi da kiyayya a kan doron kasa da mun kai ga cewa; dukkan sharri da fasadi –kamar yadda ya gabata– sun bubbugo ne daga son rai (son kai), kuma dukkan yakoki da kashe-kashe da laifuffuka da munanan ayyuka da miyagun halayen dabi’u da munanan ayyuka duk sun bubbugo ne daga son kai da yake ga mutum. Kuma da an yi maganin wannan ciwon da soyayya ta maye gurbin kiyayya, da dan’Adam ya dandani zakin soyayya. Asalin Soyayya
Mafi girman maganin son kai shi ne so saboda Allah, kuma matukar mutum ya nisanta daga tafarkin Allah, to ba yadda za a yi ya kubuta daga bautar kansa, kuma matukar yana cikin dabaibayin son kansa, to ba zai iya son waninsa ba so na hakika, don haka ne ma hadisi kudsi ya zo da cewa: “ya kai dan’Adam! Kowa yana son ka saboda kansa, ni kuma ina son ka saboda kanka[1]â€. Dukkan wanda ya yi da’awar yana son ka ya kai dan’Adam hakika yana son ka ne domin ya biya bukatarsa da kuma kare maslahar kashin kansa, kuma hakika Allah mawadaci shi kadai ne, shi ne yake son mutum domin mutum din kansa, ba don komai ba. Bisa dogaro da abin da ya gabata ne son mutum yake iya haduwa da na wasu bayan tabbatar son kansa, kuma ya cika da son Allah, don haka ne ma zamu samu yayewar sirrin da yake boyuwa bayan karfafawar musulunci ga asasin so saboda Allah, kuma ya bayyana a fili cewa wadannan da suke son mutane so na hakika kuma suke kwadaituwa a kan maslahar ‘ya’yan al’ummarsu su ne wadanda suke so don Allah saboda Allah, kuma ba komai ne ya jawo wa gurguzu rushewa a cikin da’awarsa ta kiyaye maslahar al’umma ba sai domin cewa kwadaituwa kan maslahar al’umma ba ta iya tabbata sai da fuskanta zuwa ga mahalicci, kuma wanda yake son al’umma ba don Allah ba, kuma ba ya kwadayin kare maslaharsa saboda Allah, ba yadda zai iya narkar da kansa ya ki kula da maslahar kashin kansa ta kowane hali. Hakika soyayya da ta doru a kan asasin maslahar kashin kai, a bisa hakika ba soyayya ce ga wasu ba, don haka ne ma samuwar irin wannan soyayya da dorewarta ya dogara kan maslaha ne. Duk inda aka samu cewa wannan abin da ake so ba zai iya biyan bukatar mai so ba ko maslaharsa, to sai wannan soyayya ta kau, kuma sudayawa soyayyar ta kan koma zuwa ga kiyayya, kuma wannan ne dalilin da ya sanya wannan nassosin na addini suke karfafa cewa dole ne soyayya ta kasance ta tsayu a kan asasin addini kuma kan tafarkin Allah kuma wannan ita ce soyayya guda daya wacce zata iya wanzuwa. Amma soyayyar da ta ginu a kan son kai da kuma don maslahar kai to ita wannan da gaggawa ko badade, ko bajima takan iya juyawa zuwa ga kiyayya: “masoya a wannan rana sashensu makiya ne ga sashe, sai dai masu tsoron Allah â€[2]. A cikin wannan abin da ya gabata ne, zai bayyana cewa hikimar kwadaitarwa ga soyayya saboda Allah yana kasancewa ne domin ita ce kashin bayan tsayuwar al’umma da kafafunta wanda ake fatan samu kuma babu wata hanyar samun haka sai da ita. Hikimar Kiyayya Saboda Allah
Saudayawa wata tambaya mai muhimmanci takan zo kwakwalen mutane cewa; idan musulunci yana kira ne zuwa ga kafa al’ummar da ta kafu a kan soyayya to don me ya karfafa mabiyansa a kan kiyayya saboda Allah kuma yake kwadaitar da su a kanta kamar yadda yake kwadaitar da su a kan soyayya saboda Allah yana mai la’akari da cewa wannan aiki shi ne mafficin ayyuka kuma mafi karfin igiyar imani?! Fiye da haka ma; mene ne larurar kin wasu maimakon son su? Sannan kuma shin kiyayya tana iya warware wata matsala ta al’umma? kuma shin zai yiwu ta kasance warwara ga daya daga cikinsu? A takaice dai mene ne hikimar kiyayya saboda Allah? Ma’anar Kiyayya Saboda Allah
Saboda sanin hikimar da take kunshe cikin kiyayya saboda Allah, tun farko wajibi ne mu fara sanin ma’anar wannan bayani wanda idan ya gabata kamar yadda yake, to babu wani sauran kuma larurar bayanin hikimar haka da zata rage.
|