Yan’uwantaka Don Allah



 â€˜Yan’uwantaka Saboda Allah

Hujjatul Islam Muhammad Raishahari

Hafiz Muhammad Sa’id Kano

Fasali na biyu: Karfafa Wa A Kan ‘Yan’uwantaka Saboda Allah

2 / 1

Hakika Muminai ‘Yan’uwan Juna Ne

Littafi:

“Hakika muminai ‘yan’uwa ne sai ku sulhunta tsakanin ‘yan’uwanku, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa samu rahama”[1].

“Ku yi riko da igiyar Allah gaba daya kuma kada ku rarraba, ku tuna ni’imar Allah gareku yayin da kuka kasance makiya sai ya hada tsakanin zukatanku sai ku ka wayi gari kuna ‘yan’uwan juna da ni’imarsa, kuma kun kasance a kan gefen ramin wuta sai ya tseratar da ku daga gareta, haka nan ne Allah yake bayyana muku ayoyinsa ko kwa shiryu”[2].

“Kuma idan suka tuba suka tsayar da sallah suka bayar da zakka, to su ‘yan’uwanku ne na addini, kuma muna rarrabe ayoyi ga mutane masu sani”[3].

Hadisai:

362. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: musulmi dan’uwan musulmi ne[4].

363. Al’kafi daga jabirul ju’ufi: Na bata fuska a gaban Abu Ja’afar (A.S) sai na ce: Ina fansarka da raina, saudayawa na kan yi bakin ciki ba tare da wata musiba ko wani abu ya same ni ba, har dai iyalina su gane haka a fuskata haka ma abokaina?! Sai ya ce; haka ne ya kai jabir, hakika Allah ya halici muminai daga tabon aljanna, sannan kuma sai ya gudanar da iska daga ruhinsa, don haka ne ma mumini dan’uwan mumini ne ta uba da uwa, idan wani abu na bakin ciki ya samu wani daga wadannan ruhuna a wani gari daga garuruwa, sai wannan ma ya yi bakin ciki; saboda shi ma irinsa ne[5].

2 / 2



1 2 3 next