Soyayya Don Allah



So Don Allah

Hujjatul Islam Muhammad Raishahari

Hafiz Muhammad Sa’id Kano

Bangare Na Biyu: So Don Allah

Fasali Na Farko: Karfafawa Kan So Saboda Allah

1 / 1

Wajabcin Soyayya Saboda Allah

350. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: ku so wanda kuke so saboda Allah, ku ki wanda kuke ki saboda Allah (S.W.T)[1].

351. Daga Imam Ridha (A.S) ya ce: son waliyyan Allah (S.W.T) wajibi ne, haka nan kin makiyan Allah da barranta daga garesu da jagororinsu[2].

1 / 2

Imani So Ne Da kuma Kiyayya

352. Littafin tafsirin Ayashi, daga abu ubaidataul hazza: na shiga wajen Abu Ja’afar (A.S) sai na ce: Ina fansarka da babana da babata, saudayawa shedan yakan shige ni sai inji raina ya baci, sannan sai in tuna sona gareku da kuma yankewa ta zuwa gareku sai raina ta yi farin ciki? Sai ya ce: ya kai Ziyad, kaiconka! Ai ba komai ne addini ba sai kauna!! Shin ba ka ganin fadin Allah madaukaki “Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni Allah zai so ku”[3].

353. al’kafi, daga Fudhail dan yassar ya ce: na tambayi Abu Abdullahi (A.S) game da so da ki, shin yana daga imani ko kuwa? Sai ya ce: shin akwai wani abu inami in ba so da ki ba?! Sannan sai ya karanta wannan ayar: “ya soyar da imani gareku kuma ya kawata shi a cikin zukatanku, sannan ya kiyantar da kafirci da fasikanci da sabo gareku, kuma wadannan su ne masu shiryuwa”[4].

354. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Dukkan wanda bai so a kan addini ba, kuma bai ki a kan addini ba, to ba shi da addini[5].

1 / 3

Mafi Karfin Igiyar Imani

355. Daga Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce: Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce da sahabbansa: wace igiyar imani ce ta fi karfi? Sai suka ce: Allah da manzonsa su suka fi sani, sai wasu suka ce; salla, wasu suka ce; zakka, wasu kuma suka ce; azumi, wasu kuma suka ce; hajji da umara, wasu kuma suka ce; jihadi. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce; duk abin da kuka fada yana da tasa falala amma ba shi ne ba, sai dai mafi karfin igiyar imani ita ce so don Allah da ki saboda Allah, da kuma jibintar masoya Allah da kuma barranta daga makiya Allah[6].



1 2 3 next