Hadisan manzo (SAW)Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Fifikon saurayi maiibada wanda yake bauta a kuruciyarsaakan tsohon da yake bautabayan ya manyanta kamar  fifikonmanzanni ne akan sauran mutane.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنَّ اللهَ يُحِبُّ الشّابَّ الَّذي يُفنيشَبابَهُ في طاعَةِ اللهِ عزّوجلّ

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Allah yana son bawan da yakekarar da samartakarsa wajan bin (bautar) Allah (SWT) .

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنَّ الله تَعالى يُباهي بِالشّابّ ِالعابِدِ المَلائِكةَ ، يَقولُ : اُنظُرُواإلى عَبدي! تَرَكَ شَهوَتَهُ مِن أجلي .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce :  Allah yana alfahari da saurayimai bauta ga mala’iku , yana  cewa : ku duba bawana! ya bar sha’awarsasaboda ni.

قال امام صادق عليه السّلام: قالَ رسولُ اللهِ صلّى الله عليه و آله : ليسَ مِنّي مَنِ استَخَفَّ بِالصَّلاةِ ، لايَرِدُ عَلَيَّ الحَوضَ  لا وَاللهِ .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Wanda ya wulakanta salla ba ya dagacikinmu, ba kuma zai zotafkina ba , a’a  sam Wallahi!.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: النَّظَرُ في وَجهِ العالِمِ حُبّاً لَهُ عِبادَةٌ .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Duba zuwa ga fuskar malamidomin so a gare shi ibada ne.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: خَيرُ النّاسِ منِ انتَفَعَ بِهِ النّاسُback 1 2 3 4 next