Girmama Kaburbura Masu Tsarki 2



Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Kaburburan Manzanni Da Tarihin Magabata Ma’abota Tauhidi

 Tafiye-tafiye domin bude ido zuwa wuraren da aka rufe annabawa da ‘ya’yansu wani abu ne wanda yake ba sabo ba a cikin al’umma. Wannan kuwa yana nuna cewa mabiya annabawa suna nuna kulawa ta musamman dangane da wadannan wurare, tare da gina gine-gine a kan kaburburansu suna kare su daga rushewa. A yanzu a ksashen Iraki, Palasdin, Jordan, Misra da Iran, akwai kaburburan annabawa (a.s) wadan aka yi gine-gine masu kawatarwa ta yadda kodayaushe mutane suna zuwa wurin domin ziyara. Sannan dakarun musulunci da su kai hare-hare don bude garuruwan Sham, sam ba ruwansu da wadannan kabuburan annabawa, ba ma haka ba kawai sun bar mutanen da suke hidima a wadannan wurare don su cigaba da aikinsu a wajen kamar yadda suke a da. Sannan ba su nuna rashin amincewarsu a kan hakan ba ko kankani. Idan da yin gine-gine a kan kaburburan annabawa wani aiki ne da ya haramta kuma ya shafi shirka, da wadannan dakaru da suka zo da umurnin khalifa domin bude wadannan garuruwa duka sun rusa wadannan gine-gine, amma koda wani dan karamin canji ba su yi ba ga wadannan kaburbura an cigaba da tafiyar da su kamar yadda suke kafin wannan lokaci. Sannan har zuwa yanzu wadannan gine-gine suna nan kamar yadda suke ta suke jawo hankalin al’ummar musulmi da ma duk mai bin addinan da Allah ya aiko da su.

 Sannan a farkon zuwan musulunci ma musulmai sun rufe annabinsu a cikin dakinsa, kuma babu wani daga cikin wadannan musulmai da yake tunani cewa yin gini a kan kabarin Manzo haramun ne.

 Sannan binciken littattafan tarihi da labaran tafiye-tafiyen masana addinin muslunci yana bayar da shedar cewa akwai daruruwan kaburbura a kasar da wahayi ya sauka da sauran kasashen musulmi:

1-Mas’udi wanda ya rasu 345Bh. wanda yake shahararren masanin tarihi ne, ga abin da yake cewa dangane da kaburburan imamai (a.s) da suke a “Bakiyya”yana cewa:

“A bisa kaburburansu a akwai dutse wanda aka rubuta: Da sunan Allah mai rahma mai jin kai, godiya ta tabbata ga Allah wanda yake kashe al’umma yake kuma raya matattu. Wannan shi ne kabarin Fadima “yar manzon Allah (s.a.w) wadda take ita ce shugabar matan duniya. Da kabarin Hasan Bn Ali Bn Abi Dalib da kabarin Ali Bn Husain Bn Ali Bn Abi Dalib da kabarin Muhammad Bn Ali Bn Husain Bn Ali Bn Abi Dalib da Kabarin Ja’farus Sadik Bn Muhammad”. [1]

 Mas’udi ya kasance daga cikin masana tarihi na karni hudu Bayan hjira. ’Yan salafiya wadanda suke da kankamo sun tafi a kan cewa; wannan karni da karnonin da suke kafinsu su ne fiyayyun karnonin tarihin musulunci, sannan ayyukan da suka yadu a tsakanin musulmi a wannan zamani suna nuna kasantuwar abubuwan da shari’a ta yarda da su. Amma abin bakin ciki wannan babban dutse wanda Mas’udi yake fada wanda aka yi wannan rubutu a kansa, sakamakon rushewar da wahabiyawa suka yi wa “Bakiyya” yanzu babu shi a samuwa. Saboda haka yanzu wadannan kaburbura ba a iya bambance su.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 next