Girmama Kaburbura Masu Tsarki



Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Al’ummun da suke raye a kasashen da suka cigaba a duniya zaka ga suna kokarin wajen kare kayan tarihi kuma suna nuna soyayyarsu ga wadannan abubuwa na tarihi. Sannan suna iya kokarinsu da su kare wadannan kayan tarihi don kada su bata ko su lalace. Domin kiyaye wadannan kayan tarihi kuwa wadanda suke nuna cigabn su a tsawon tarihi har ma’aikatu na musamman suka samar da ma’aikata kwararru domin kawai wannan aiki. Sakamakon haka ne ba su ba da wata dama da zata sanya wani guntun abu daga cikin wadannan kayan tarihi da suka hada da wani allo wanda aka yi wani rubutu a kai ko guntun jirgin ruwa da ya bata. Domin sun yi imani da cewa wadannan kayan tarihi suna ba da wata sheda ce ta musamman ta su wadannan al’umma. Mutanen da suka yanke daga al’ummarsu da manyan tarihinsu da suka gabata suna da hukuncin yaro ne wanda ya bata daga hannun iyayensa.

 Cigaban musulunci wani cigaba ne wanda yake mai girman gaske wanda a karnoni na tsakiya shi ne kawai cigaban da babu kamarsa. Musulmai sakamakon koyarwar da suka samu daga littafinsu na sama, sun kafa cigaban da ba a taba yinsa ba a tarihi. Wanda ya kai kololuwarsa a cikin karni na hudu, ta yadda gabas da yammacin duniya suka shaida haka, kamar yadda ya gina Tajmahal na kasar Indiya da Kasar (Spain) sauran gine-gine masu ban al’ajabi, wanda ta hanyar kaitsaye ko kuma ba kaitsaye ba. Kamar yadda masana na yamacin duniya suka tabbatar da cewa cigaban yammacin duniya ya samu asali ne ta hanyar Andulus ko kuma ta hanyar yakin da ya auku tsakanin musulmi da kiristocin yammacin duniya.

 Cigaban musulunci ya fara ne da aiko manzon Musulunci (s.a.w) ko kuma da wata ma’ana ya fara ne da haihuwar shi manzon, Sannan da taimakon mabiyansa ya cigaba ta kafuwa da yaduwa a sauran sassan duniya. Gine-ginen da suke dangane da Manzo ko kuwa wasu daga cikin sahabbansa suna daga cikin wannan cigaba na musulunci. Sannan kuma wannan ba mallakin wani ba ne ta yadda zai yi abin da ya ga dama da su, wannan na dukkan al’ummar musulmi ne. Saboda haka babu wata hukuma ko wasu mutane da zasu yi abin da suka dama da wannan kayan tarihi da cigaban musulunci ba tare da izinin sauran musulmi ba, ta yadda ta hanyar yaki da bidi’a da tsayar da tauhidi su kawar da wadannan kayan tarihi.

 Tarihin musulunci yana gaya mana cewa: An haifi manzon musulunci ne a shekara ta 570 bayan haihuwar Annabi Isa (a.s) Sannan bayan ya kai shekara 40 da haihuwa aka aiko shi a manzanci, bayan aiko shi da manzanci ya yi shekara 13 a garin Makka yana isar da wannan sako. Bayan wannan ne tare da umarnin Ubangiji ya bar inda aka haife shi zuwa garin Madina, Inda a can ne ya yi shekara 10 yana isar da wannan sako na musulunci kuma ya yi fito na fito da mushrikai makiya musulunci, sakamkon bayar da shahidai da ya yi a wannan hanyar ya samu damar daga tutar musulunci a dukkan yankin kasashen Makka da kewayenta (yanki mai girma daga cikin Jaziratul Arab) A shekara ta 11 bayan hijara ne ya koma zuwa ga rahamar Ubangijinsa, sannan bayan wafatinsa sahabbansa suka cigaba da wannan aiki na yada musulunci a sassan duniya daban-daban.

 Wannan kuwa ya shafi rayuwar da kokarin Manzo da iyalansa da da mabiyansa ne (kamar yadda muka fadi cewa shi ne tushen wannan cigaba) Saboda haka dole mu yi kokari wajen kare wannan asali.

Kaburburan Shugabannin Addinin Musulunci Suna Nuna Tarihin Musulunci

 Dole ne mu kula da cewa duk wani abu da zai faru a wani zamani yana kore duk wani shakku ga wadanda suke rayuwa a wannan zamani. Amma tare da gushewar zamani sakamkon ko-in-kula na mutane zai sanya wannan yakini da tabbas da yake ga mutane ya ragu. Ta yadda a hankali zai zama ana shakku da tararrabi a kan faruwar wannan abin, ta yadda wani lokaci ma zai koma kamar wata tatsuniya. Abubuwan da suka faru ga addinan da suka gabata a lokacin da suka faru babu wani shakku ko tardidi a kan faruwarsu, amma sakamakon rashin kulawa a yau sun zama kamar tatsuniya.



1 next