Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w)Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Ziyarar Kabarin dukkan musulmai da musamman ziyarar kabarin Manzo wani abu ne Wanda yake mustahabbi mai karfi a cikin musulunci. Sannan malaman hadisai daga Sunna da Shi’a sun ruwaito hadisai da dama a kan mustahabbancin ziyarar kabarin Manzo wadanda wasu daga cikinsu sun gabata a cikin bahasin da ya gabata ta yadda babu wani malami daga cikin malaman musuluncin da ya ba wa kansa damar yin shakku a kan mustahabbancin ziyarar Manzo. Wannan kuwa ya hada har da Muhammad Bn Abduh wanda yake da wasu masatlolin dangane da abin da ya shafi annabawa, a nan ba kawai ya yi shiru ba ne, sai dai ya yi magana a kan mustahabbcin ziyarar Manzo (s.a.w). Sannan mun kawo abin da yake cewa dangane da hakan a bahasimmu na baya.

 Tare da la’akari da kasantuwar mustahabbicn ziyarar Manzo, amma msulmi sun kasu akan wannan kyauata ta Ubangiji:

1-Mazauna Madina

Mazauna Madina sakamakon makwabtaka da suke da ita da Manzo (s.a.w). Suna iya ziyartarsa ba tare wata wahala ba don aiwatara da wannan mustahabbi.

1-Mazauna sauran wurare a cikin duniya

Mazauna sauran sassan duniya dole ne su yi tafiya domin su damar yin sallama ga kabarin Manzo Su ce”Amincin Allah ya tabbata a gareka ya manzon Allah”

 A nan tambayar da zata shi ne menene hukuncin wannan tafiya a shari’a?1 2 3 4 5 6 7 next