Bidi’a A Cikin AddiniMawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Tauhidin Annabi Ibrahim wanda yake shi ne tushen duk wani addini da yazo daga sama, yana da matakai daban-daban wadanda masu ilimin kalam suka yi cikakken bayani a kansu, sannan su yi rubutu da dama a kan hakan.

Daya daga cikin wadannan matakai kuwa shi ne (kadaita Allah a cikin kafa doka da hukunci) wato Allah ne kawai yake da hakkin kafa doka da bayar da umarni ga halittunsa. Sannan babu wani wanda yake da hakkin ya kafa wa wata al’umma doka sannan ya tilastawa mutane a kan su yi aiki da wannan dokar, ta yadda zai takaita ‘yancin mutane. wajibi ne kuma tilas ne ga kowane mai kadaita Allah ya yi imani da cewa babu wanda zai kafa doka ko shari’a sai Allah madaukaki. Kuma shi kadai ne yake da iko a kan mutane da dukiyoyinsu. Sannan shi yake da iko a kan umarni da hani.

Wannan al’amari kuwa ana iya tabbatar da shi ta hanyoyi guda biyu wato ta hanyar hankali da shari’a, a nan zamu fara tabbatar da hakan ne ta hanyar hankali.

Takaita kafa doka ga Allah kawai bai zamo sakamakon karamin tunani ba ne, domin kafa doka ingantacciya yana da sharudda na shi na kansa, wannan sharudda kuwa ba za a iya samun su ba a ko’ina sai wurin Allah madaukaki. Wadannan sharudda kuwa su ne kamar haka:

1- Dole ne wanda zai kafa doka ya zamana ya san mutum hakikanin sani.

2-Sannan kada ya zamana akwai wani amfanin da zai dawo zuwa ga mai kafa dokar.

3-Ya zamana ya tsarkaka daga duk wani neman matsayi ko daga wani bangarenci na wata kungiya.1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next