Iyakokin Tauhidi Da Shirka A Cikin IbadaMawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani
Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani
Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Halittar Mutum da duniya baki daya wata hikima ce ta Allah wanda yake masani kamar yadda duk wani aiki na shi mai hikima yana tattare da wata manufa tasa, wanda wannan manufa kuma daga karshe tana komawa ne ga kan shi abin halitta, ba wai zuwa ga mahalicci ba kamar yadda muka sani cewa shi mawadaci ne ba ya bukatar komai wato amfanin halittar yana komawa ne zuwa ga bayinsa. Gaskiyar wannan al’amari kuwa yana iya bayyana karkashin wadannan abubuwa guda biyu masu zuwa:
1- Allah mawadaci ne marar iyaka saboda haka ba shi da wata bukata zuwa ga komai.
2- Allah mai hikima ne don haka dole ne hikimarsa ta bayyana a cikin ayyukansa, wato dole ne ayyukansa su tsarkaka daga duk wani rashin hadafi da manufa.
Tare da kula da wadannan asali guda biyu da muka ambata a sama zamu isa zuwa ga sakamakon da yake nuna mana cewa Allah madaukaki bai halicci mutum da duniya ba sai tare da manufa ba, Allah mdaukaki ya halicci mutum da duniya baki daya domin wata manufa da amfani wanda kuma wannan amfani yana komawa ne ga su abin halittarsa. A kan wadannan ka’idoji ne guda biyu Allah yake fada a cikin Kur’ani mai girma cewa:
“Shin mutane suna tsammanin mun yi halitta ne haka nan babu wata manufa, sannan kuma ba zaku koma zuwa garemu ba”.
A nan wannan tambayar zata zo ga zukata cewa to shin menene manufar halittar mutum? A wajen amsar wannan tambayar a takaice muna iya cewa: Sanin Allah da siffofinsa kyawawa, da kuma siffatuwar ruhin mutum da wadannan siffofin wadanda su ne ake cewa kyawawan dabi’u wadanda suke kunshe a cikin ruhin ‘yan Adam daga nan muna iya fahimtar manufar halittar shi mutum.
Domin kuwa sanin Allah yana tattare da wani nau’i ne na samun alaka da wata cibiya ta kamalar mutum. Sannan siffatuwar mutum da wadannan siffofi masu kyau wani nau’i ne na bayyanar ‘yan adamtaka na mutum, kuma wata alama ce da take nuna cewa ya isa zuwa ga kololuwar kamalar da yake iya samu.
Mutum yana da wasu makamai da zai iya amfani da su domin samun kammala, wadannan makamai kuwa su ne kamar haka:

A: Tarbiyar Kyawawan Dabi’u
Allah madaukaki ya halicci mutum kuma ya sanya masa son Allah da siffantuwa da siffofin kammala da kyamar siffofin da ba su da kyawu, wannan abin da mutum yake ji kodayaushe yana sanya masa wata natsuwar ruhi da samun alaka da Ubangiji a kowane lokaci, sannan ilimin yau da kullum wadanda suke karkata zuwa ga addini wadanda kodayaushe suna kara sanya wa mutum komawa zuwa ga duniyar gaibu da kwadayi zuwa ga kyawawan siffofi wadan su ne ake cewa kyawawan dabi’u, duk yana nuni ne ga wannan al’amari. A hakikanin gaskiya wannan abin da mutum yake ji a cikin ruhinsa na karkata zuwa ga kyakkawa wani jari ne ga shi mutum wanda sakamakon tarbiyarsa, sai mutum ya kara samun kammala, sannan kuma idan mutum ya rasa wannan sai mutum ya ja baya ya kuma yi nisa da samun kamala.
B: Hankali
Hankali da tunani fitila ce ga mutum wacce take haska masa domin isa zuwa ga kamala. Sakamakon amfani da wannan haskakawa ta hankali mutum zai iya gane hanyar isa zuwa ga kamala, sannan kuma ya kama hanya domin isa zuwa ga kamalar.
C: Annabawa Da Manzannin Allah
Annabawa da manzannin Allah sun kasance sun zo da duk abubuwan da zasu iya kai mutum zuwa ga kammala da cin nasara, suma matsayin wani jari ne na uku wanda mutum zai iya amfani da shi domin ya samu cin nasara da kammala, sannan wani bangare na koyarwar annabawa shi ne tarbiyantar wannan halittar da mutum yake da ita ta son kyawawan dabi’u da kusantuwa zuwa ga Allah. Kai sun kasance kamar kwararen mai binciken kasa da yake amfani da na’urori domin fito da abin da yake so daga cikin kasa. Wadannan abubuwa da Allah ya halitta wa mutum sakamakon koyarwar annabawa ne zai bayyana.
Imam Ali (a.s) yana bayyanar da wannan hakika inda yake cewa: “Allah madaukaki ya aiko da annabawa domin su bukaci mutane a kan su cika alkawarin da suka dauko daga Allah, sannan su tuna ni’imomin da suka manta da su, sannan su farkar da tunanin da ya faku”. 
Wannan alkawura kuwa su ne wadannan halitta da Allah ya yi wa mutum na karkata zuwa ga Allah da kyawawan dabi’u. Don haka halittar mutum tana tattare da wannan nau’i na halitta wacce take wani alkawari ne da Allah ya dauka da mutane.
A cikin wadannan abubuwa kuwa da Allah ya halittacikin zatin mutum akwai kadaita bautar Allah madaukaki kuma yana daga cikin muhimmansu. Gaskiyar al’amari ma wannan shi ne sakon dukkan manzanni da annabawa domin kuwa muna iya takaita dukkan ayyukansu a kan kira zuwa ga kadaita Allah (Tauhidi) kamar yadda yake cewa:
“Hakika mun aika Manzo a cikin kowace al’umma a kan a bauta wa Allah shi kadai, sannan a guji biyayya ga dagutu (duk abin da ba Allah ba).  Kula da ma’anar wannan aya zamu iya gane muhimmancin tauhidi ko kadaita Allah da kore duk wani wanda ba Allah ba a cikin bauta, shi ne kuma muhimmin sakon da Allah ya aiko manzanninsa da shi zuwa ga al’ummarsu kuma zamu ma iya takaita dukkan ayyukansu a cikinsa. Sannan kuma dukkan addinan Ibrahimiyya kira ga tauhidi shi ne a sama wajen da’awarsu.
Duk da cewa a cikin tsawon tarihi an yi kokari domin karkatar da wannan asali wato tauhidi ta yadda har ya zamana ana bautar mutum kamar yadda mutanen annabi Isa (a.s) suka sanya matsayin abin bauta a garesu, Amma masu tsarkin zuciya daga mabiyan dukkanin addinan da Allah ya aiko ba su manta da wannan asali ba na tauhidi da kadaita Allah a wajen bauta, sun dauke shi wani abu wanda yake babu kokwanto a cikinsa. A kan haka ne ma Allah yake ce wa cikamakon manzanninsa (s.a.w) wajen tattaunawarsa da kiristoci da mabiya wasu addinai cewa ya kira su zuwa ga kadaita Allah kamar haka: “Ka ce ya ku ma’abuta littafi ku zo zuwa ga kalmar da ta daidaita tsakaninmu cewa kada mu bauta wa kowa sai Allah sannan kada mu hada shi da kowa, sannan kada mu riki wasu daga cikimmu a matsayin abin bauta sabanin Allah, idan kuwa suka juya sai ku ce musu to ku sheda mu musulmi ne”.

Matakai Hudu Na Tauhidi
Tauhidi shi kansa yana da matakai daban-daban, kamar tauhidi a cikin bauta wanda dukkan annabawa sun hadu a wajen kira zuwa ga hakan wanda kuma yake kuma yana daya daga cikin rassan tauhidi na musamman. Sannan a takaice zamu yi bayani a kan sauran sassan tauhidi kamar haka:
A-Kadaita Allah a cikin zatinsa: wato yin imani da cewa Allah shi kadai yake kuma ba wasu abubuwa suka hadu suka yi shi ba (Tauhidi Ahdi da wahidi).
B-Kadaita Allah a cikin yin halitta: Yin imani da cewa babu wani mai halitta sai Allah madaukaki kuma ba ya bukatar taimakon kowa wajen yin hakan.
C-Kadaita Allah a wajen tafiyar da al’amura: Halitta da tafiyar da duniya duk yana hannun Allah, domin kuwa shi ne ya halitta mutum da duniya baki daya, don haka shi ne yake da hakkin tafiyar da ita. Wadansu da suke da hannun wajen tafiyar da duniya dukkansu suna yin hakan ne da izini da umurninsa.
D-Kadaita Allah A Cikin Bauta: Wato yin Imani da cewa babu abin da ya cancanta a bauta wa sai Allah, sannan duk wanda ba shi ba bawansa ne kuma mai rauni ne, Saboda haka dole ne kowa da komai su mika wuya zuwa ga Allah.
A dukkan cikin matakai na kadaita Allah, mataki na karshe ne a nan zamu yi magana a kansa domin shi ne maudu’in bahsinmu, saboda muhimmancin na musamman yake da shi.
Kamar yadda muka ce kadaita Allah a cikin bauta shi ne abin da zamu yi magana a kansa, ba wai yana nufin cewa akwai shakku a cikinsa ba ne ta yadda zamu yi kokari domin gusar da wannan shakku. Domin kuwa kamar yadda muka yi bayani a baya wannan asali wani karbabben abu ne ga dukkan addinai da suka zo daga Allah kuma sun hadu a kan wannan take suna masu cewa “Kai kwai muke bauta”.
Kai ba za a iya kiran mutum musulmi ba sai idan ya amince da wannan asali na kadaita Allah a cikin bauta, domin kuwa kin amincewa da wannan yana daidai da kin amincewa da musulunci baki daya.
Sannan idan muka manta da amincewar dukkan musulmi a kan wannan asali na kadaita Allah a cikin bauta, duk da cewa dukkansu sun hadu a kan wannan asalin. Halarcin wasu abubuwa kamar neman ceto daga annabawa ko kuma yin taro domin girmama ranar haihuwarsu da makamantan wadannan idan muka sanya a matsayin abin da zamu yi Bahasi a kansu, domin kuwa wasu daga cikin musulmi suna ganin cewa wannan shirka ne a cikin bautar Allah saboda suna ganin cewa neman ceto daga wani annabi ko kuma girmama ranar haihuwarsa wani nau’ ne na bautarsa.
Saboda haka a nan dole ne mu tantance hakikanin wannan girmamawa da muke yi wa Manzo a ranar haihuwa ko kuma neman wani abu da ake yi daga manzannin, ta yadda zamu iya gane shin wannan bauta ce ta yadda zai iya zama shirka ko kuwa kawai girmamawa ce ba tare da an bauta masa ba, ta yadda zai iya zama halas kuma ma mustahabbi.
Wannan kuwa yana iya yiwuwa ta sakamakon bayyana hakikanin ibada a ilimince, ta yadda duk inda muka ga ibada zamu iya ganewa da kuma abin daba ibada ba ne. Sannan mu iya bambamce girmamawa da kuma ibada, Domin kuwa idan ba a bayyanar da hakikanin ibada ba, to ba za iya yin hukunci ba a cikin irin wadannan wurare.
Ma’anar Ibada
Bayyanar da ma’anar kowane abu dole ne ya kasance a takaice kuma ta yadda zai kunshi dukkan ma’anar abin ya kuma hana wani abu wanda ba shi ba shiga cikin ma’anar. wato ta yadda zai iya tattaro duk wani abu wanda yake cikinsa sannan yak ore duk wani abu wanda ba ya a cikinsa. Wato ta yadda za a iya bayar da wata ka’ida wacce zata iya sanyawa a gane abin da yake ibada da kuma abin da ba ibada ba ne. Saboda haka idan muka samu irin wannan ka’ida zata taimaka mu warware da yawa daga cikin matsalolin damuke fuskanta dangane da ibada da abin da ba ibada ba.
Muna iya fahimtar ma’anar ibada ta hanyoyi guda uku kamar haka:
A-Tahanyar komawa zuwa ga kamus.
B-Ta komawa zuwa ga wuraren da a ka yi amfani da kalmar ibada.
C-Bambance hakikanin ibadar masu kadaita Allah da kuma masu bautar gumaka.
Fadakarwa a kan bin da muka fada a sama kuwa shi ne a cikin hanya ta farko ba zamu iya samun ka’ida ba wacce zata taimake mum u iya gane menene hakikanin ibada. Saboda haka hanya ta uku ce kawai zamu iya bi domin mu gane mene hakikanin ibada. Amma dai zamu yi magana a kan kowace daya daga cikin hanyoyin.
A-Komawa Zuwa Ga Littattafan Lugga (Kamus)
Daya daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen gane ma’anar ibada ita ce yin amfani da Littattafan lugga wato kamus din kalmomi. Ibn Manzu a cikin littafinsa na lugga wato lisanul arab yana cewa: Ibada ita ce nuna kaskantar da kai da tawalu’u.
Amma Ragib a cikin mufradat ya yi bayani da cewa lafazin ibada yana nuni zuwa ga kaskantar da kai da girmamawa amma fiye da abin da aka ambata a baya, wato ibada nuna kaskantar da kai ne na karhse.
Amma Kuyud abadi a cikin Kamus yana cewa Ibada ita ce biyayya kuma Ibn Faris yana karawa da cewa, ibada ita ce nuna tausasawa da kuma kaskantar da kai. 
Wannan ma’anoni ba zasu iya bayyanar da hakikanin ma’anar ibada ba, domin kuwa bayyanar da kaskantar da kai ko kuwa marar iyaka ne, ba ya zama ibada, ta yadda idan mutum ya yi hakan ga wanin Allah ya yi shirka. Domin kuwa nuna kaskantar da kai da girmamawa ga iyaye wani abu ne wanda yake mai kyau kuma wani umarni ne ma da shari’a ta yi a kansa, amma ba yana nufin ana bauta musu ba. Kamar yadda Allah madaukaki yake cewa: “Ka kaskantar da kafadunka zuwa gare su domin tausayi da girmamawa”.  Sannan Allah madaukaki a cikin Kur’ani mai girma yana umurtar Mala’iku da su yi wa Adam (a.s) sujjada, sannan Annabi Yakub da ‘ya’yansa sun yi wa Annabi Yusuf sujjada.
Saboda haka idan muka takaita kalmar ibada da ma’anar girmamawa da kaskantar da kai to muna iya cewa mala’iku sun bauta wa Adam haka nan Annabi Yakub da ‘ya’yansa sun bauta wa Yufus (a.s) (muna neman tsari a kan hakan) wato sun bauta wa wanin Allah kuma wannan ya mai da su sun yi shirka da Allah, sannan kuma Allah ya yi umarni da a bauta wa waninsa…
Wannan kuwa a fili yake babu wani mai tauhidi da yake iya fadar wannan magana. Saboda haka daga nan zamu iya gane cewa bayyanar da ma’anar ibada da aka yi a sama da cewa girmmawa da kaskantar da kai, ya shigo da abin da yake ba ibada ba ne, don haka ba ya bayyanar da hakikanin ma'anar ibada.
Mai yiwuwa a yi tunanin cewa ai Adam yana matsayin kibla ne amma sujjada an yi wa Allah ne madaukaki, amma wannan tunanin ya sabawa zahirin ayar Kur’ani mai girma. Domin kuwa idan haka ne babu ma’anar bijirewar da shaidan ya yi inda Allah yake cewa: “Zan bauta wa wanda ka halitta da yumbu sujjada?”
Amma abin da muka fada ba yana nuna rashin girma aikin da marubuta Littattafan lugga ba ne, domin kuwa manufar su shi ne, bayyanar da ma’anar kalma a takaice, ba wai bayyanar da ma’anar kalma ba a ilimince. Yanzu kuwa zamu ci gaba da bayani a kan hanya ta biyu:
B-Bincike A Kan Wuraren Da Aka Yi Amfani Da Kalmar Ibada
Bincike kuwa a kan wuraren da aka yi amfani kalmomin ibada shi ma ba zai iya bayyanar mana da hakikanin ma’anar ibada ba, wato ba zai iya ba mu wata ka’ida ba ta yadda zamu bambance abin da yake ibada da wanda ba shi ne ba. Domin kuwa sakamakon takaitawar da ake yi wajen amfani da kalmomin a cikin adabin larabci ko kuma aron kalma da ake yi, tabbas ba zai bayyanar da ma’anar ibada ba ta yadda zai iya zama shirka idan a ka yi shi ga wanin Allah. Misali a kan ce wa mutumin da yake da cin abinci da yawa ko kuma mai son makami da suna bawan ciki ko mai bautar makami. Amma kowa ya sani cewa a wadannan ma’anoni wadanda ake amfani da su wajen mai cin abinci da yawa ko mai son makami ba suna nufin hakikanin ibadar da muke nufi ba a nan. Amma sakamkon wadannan mutane duk sun mayar da gurinsu wajen wadannan abubuwa shi ne ya janyo mutane suke cewa suna bautar wadannan abubuwa da aka ambata a sama. Haka nan ma Kur’ani mai girma ya yi amfani da wadannan kalmomi a wurin da ba suna nufin ma’ana ta hakika ba ne, inda yake cewa:
“Ya 'yan Adam yanzu bai dora alkawari a kanku ba cewa kada ku bauta wa Shaidan, domin kuwa shi makiyi ne a gareku?”
Mutane da suka nutse wajen bin sha’awace-sha’awacen duniya da fushi suna masu bin shaidan ne, amma yin amfani da kalmar ibada a nan wani nau’i ne na aron kalma da yin amfani da kalma a wajen da ba hakikanin ma’anarta ba ne. A nan an yi haka ne ta yadda za a gargadi masu yin wadannan ayyuka ne kawai. Amma babu wani lokaci da za a iya kiran mai karya ko mai bin sha’awarsa da mai bautar shaidan, ta yadda zai iya zama daya da mushirikai.
Saboda haka bin wadannan hanyoyin biyu duk da cewa ba za a ce ba shi da wani amfani ba, amma ba zai isar da mu ba zuwa ga abin da muke nema na bayyanar da hakikanin ibada. Saboda haka dole ne mu bi hanya ta uku domin mu samu abin da muke nema.
 
C-Bincike A Kan Hakikanin Siffofin Ibada
A cikin hakikanin Ibadar da masu kadaita Allah ko masu bautar gumaka suke yi muna iya haduwa da wasu siffofi na ibada guda biyu, kamar yadda muna ganin duka wadannan guda biyu suna yin bauta ne. Wadannan alamomi kuwa sun kasu gida biyu wato na zahiri da na boye, wadannan alamomi guda biyu kuwa, sun kasance kamar oksijin da haidurojin ne a wajen ruwa, wato abin da suka hadu suka ba da hakikanin abin da ke ruwa, suma wadannan alamomi na ciki da na waje haka suke a wajen ibada, domin kuwa su ne suke bayyanar da hakikanin ibada da abin da ba ibada ba.
Alama ta farko kuwa wacce a cikin kowace ibada muna ganin wannan a zahiri shi ne, kaskantar da kai da girmamawa wanda ake bayyanar da shi da gabobi da harshe. Amma a nan ibada da girmamawa duk abu guda ne. Saboda haka dole mu tafi domin gano alama ta biyu wacce take bambace hakikanin ibda da abin yake kama da ita ta yadda zamu iya isa hadafinmu na asali.
Wannan alama ta biyu kuma alama ta ciki ita ce, wacce take sanya mai ibada ya kaskantar da kansa a gaban wanda ya halitta shi da nufin yi masa bauta ta yadda zai kawar da duk wani abu na jin kansa kawai yana kallon mahaliccinsa ne, ta yadda ta hanyar harshensa da duk gabobinsa yake bayyanar da wannan kaskantarwa.
Amma sanin hakikanin wannan al’amari yana samuwa ta hanyar niyyar da ta sanya a ka aiwatar da wannan na’u’i na girmamawa da kaskantar da kai wanda yake bayyanar da mushirikai da kuma masu kadaita Allah madaukaki. saboda haka idan muka gano wadannan dalilai da suka sanya aka yi wannan aiki to zai zame mana sauki mu iya gane ibada da kuma abin da yake ba ibada ba.
Dalilan masu kadaita Allah wajen yin wannan ayyuka na kaskantar da kai, yana da alaka gwargwadon saninsu da Allah abin bauta da kuma imaninsu da tsarkake shi. Wadannan niyyoyi nasu kuwa na cikin zuciya muna iya kasa su zuwa gida biyu kamar haka:

Manufar Arifai A Kan Ibadar Ubangiji
Manufar arifai da sufaye a kan bautar Allah shi ne tsananin nuna soyayyarsu ga Allah mahalicci. Wato sanin hakikanin kyawon Ubangiji shi ne yake fizgo dukkan samuwar zuwa ga abin kaunarsu ba tare da la’akari da ladar da zasu samu wajen bautar ba ko ba tare da tsoron wata azaba ba suke bautarsa. Wato; so da kaunar Mahalicci da kyawawan siffofinsa ne suke fizgo su zuwa ga kaskantar da kai da girmama shi da bautarsa.
Ya zo a cikin Hadisai inda ake kiran wannan nau’i na ibada da ibadar masu ‘yanci wacce take ta tsarkaka daga duk wani nau’in bukatar zuci. Kamar inda yazo cewa: “Wasu mutane sun bauta wa Allah kawai don soyuwa zuwa gareshi, wannan ita ce “Ibadar ‘yantattu”
Wannan manufa ta ibada kamar yadda aka yi bayani a sama ba manufa ba ce wacce ta hada kowane mutum a kanta, ba dukkan masu kadaita Allah ake samunta ba. Kawai ana samunta ne ga wasu mutane na musamman wadanda suka isa zuwa ga wani mataki na kamalar dan Adam, wato ba su da wata manufakan yin ibada sai kawai son abin bauta da siffofinsa kyawawa. Saboda haka a nan dole ne mu yi bayani a kan alamomin ibada da suka hade kowane mutum.
Manufar Bautar Da Mutane Suke Yi Wa Allah
Wannan manufa kuwa ita ce wacce take sanya mafi yawan masu kadaita Allah suke yin bauta Allah madaukaki, wannan kuwa ya samo asali ne ta yadda suke kallon Allah ta wasu siffofinsa guda biyu kamar haka:
A-Shi ne yin imani da cewa Allah shi ne mahaliccin Mutum da duniya baki daya sannan duk wani abu nasa yana zuwa ne daga Allah.
B-Bayan yin imani da cewa Allah shi ne Mahaliccin duniya da abin da yake cikinta, sun yi imani da cewa Allah madaukaki shi ne yake tafiyar da duniya baki daya, ba wai Allah ya halicci duniya ba sai ya bar tafiyar da ita a hannun waninsa. Abin ba haka yake ba, Allah shi ne ya haliici duniya kuma shi ne yake tafiyar da rayuwar dan Adam a nan duniya da lahira. Sannan duk wata bukata da mutum yake da ita babu wani mai iya biya masa ita sai Allah shi kadai, saboda haka Allah shi ne yake warware dukkan matsaloli sannan kuma mai amsa kiran masu bukatar taimai konsa.
Kur’ani mai girma shi ma yana bayar da shaida a kan wannan al’amari, domin kuwa bayan ya yi magana a kan cewa Allah mahalicci ne to yakan tabbatar da cewa shi ne kuma yake tafiyar da duniya, sannan sai ya yi umurini da bautar Allah. Sakamakon wannan jeri da muka gani sama muna iya cewa bautar Allah sakamakon abubuwa guda biyu ne wadanda mutum yake da masaniya dangane da Allah a kansu, wato kasancewar Allah mahalicci kuma mai tafiyar da duniya. Kamar yadda yake cewa:
“Lallai ubangijinku shi ne wanda ya halicci sammai da kasai, sannan ya daidai a kan mulki yana tafiyar da al’amura babu wani mai ceto sai da izininsa, wannan shi ne ubangijinku, ku bauta masa, me ya sa ba ku tunani”.
A cikin wannan aya abubuwa guda hudu suka zo kuma suna bin juna:
A-Lallai ubangijinku shi ne wanda ya halicci samai da kasai.
B-Shi ne yake tafiyar da al’amura.
C-”Babu wani mai ceto sai da izininsa”. 
D-Wannan shi ne Ubangijinku, to ku bauta masa. Sannan duk tasirin wani abu yana faruwa ne da izininsa, saboda haka ku bauta wa wanda yake shi ne mawadaci marar iyaka.
Mutanen masu kadaita Allah wadanda suka samu tarbiya a makarantar annabci shi ne ya sanya suka yi sauri wajen sanin cewa Allah shi ne mahalicci kuma mai tafiyar da duniya sannan babu wani mai tasiri a cikin duniya sai Allah ko kuma tare da izininsa, wannan shi ne ya sanya suka sunkuya zuwa gare shi domin girmamawa, sannan ba su neman biyan bukatarsu sai wajensa domin shi ne kawai yake iya biya musu bukatarsu, sannan sakamakon bin umurninsa ne suke samun yardarsa. Sannan babu wani mai tasiri a cikin rayuwa sai shi kadai, saboda haka ne ba su neman komai ga wani sai shi madaukaki. Sannan duk wani abin halitta wanda ba Allah ba kodayaushe yana fadar cewa “Ni ban mallaki komai ba ga kaina na amfani ko mai cutarwa sai kawai abin da Allah ya so”.
Manufar Mushirikai A Kan Bautar Gumaka
Babu shakka a kan cewa mushirikai suna girmama gumaka ne a kan matsayin bauta duk da cewa wani abu wanda yake bai inganta ba kuma ba shi da wani amfani.
Yanzu dole ne mu ga menene dalilansu a kan bautar wadannan gumaka. Amma kafin mu ci gaba da bayani a kan dalilansu a kan bautar gumaka, ya kamata mu yi bayanin a kan nau’o’i da matakai na shirka. A nan muna iya kasa mushirikai zuwa gida biyu kamar haka:
A-Wadanda suke bautar wanin Allah ko kuma suke hada Allah da wani sun yi imani da cewa Allah wanda ba shi da farko kuma ba shi da karshe ya bayyana ne a abubuwa guda uku, kamar yadda yake a addinin Hindu ya tafi a kan wadannan abubuwa guda uku kamar haka:
1-Barahama: Wanda yake halitta.
2-Wishno: Wanda yake tsare al’amura.
3-Sifa: Wanda yake hallakar da abubuwa.
Bayan karni shida da haihuwar Annabi Isa (a.s) an samu canji a cikin akidun “Barahnama” Wanda ya sanya aka samu wani addini mai suna addinin “Hindu”A cikin wannan akida, Allah wanda yake ba shi da farko ya bayyana ne a abubuwa guda uku, wanda muka yi nuni a kansa a sama.   Sannan yanzu akwai Salus (mai tsarki) mai siffar kawuna guda uku wanda masu addinin hindu yanzu haka sun sanya shi a wani wuri da ake gani har yanzu yananan.
Abin bakin ciki kiristoci ma a karnoni biyar na kiristanci, sakamakon janyo wasu abubuwa daga falsafar Girka da na gabacin duniya zuwacikin addininsu, sai suka shiga cikin hadarin ukunta Allah, sakamakon haka ne ukunta Allah sabo ya zo da sunan uba da ruhul kuds. Haka yana cewa hakikanin Ubangiji yana bayyana ne ga abubuwa guda uku madaidaita, wato Allah uba Allah da Allah Ruhul Kuds, zuwa inda yake cewa: Amma wannan Bayyana guda uku daraja guda ce da aiki. 
A nan abin da muke so mu sani kuma mu yi bincike a kansa shi ne shirka da yadda ta kasance a kasashen larabawa yayin da Kur’ani ya sauka da kuma yadda yake magana a kan wannan shirka, sannan a wannan zamani namu wadanda suke magana a kan shirka da tauhidi suna nufin wannan shirka ne.
Larabawa ba su kasance suna inkarin Tauhidi a cikin halitta ba, dukkansu sun yi imani da cewa Allah shi ne mahaliccin sammai da kassai da mutane. A kan haka ma Kur’ani ya yi magana a cikin ayoyi da dama.
Saboda haka shirkarsu ta kasace a cikin abubuwa guda biyu ne wato shirka a cikin tafiyar al’amura yayin da suke ganin cewa wasu abubuwa ne (gumaka) suke tafiyar da duniya wato Allah ya bar musu al’amarin tafiyar da duniya ko kuma ya ba su wani bangare na yin hakan, duk da cewa sun tafi a kan cewa Allah shi ne mahaliccin duniya da abin da yake cikinta.
Masu rubutu a kan akidoji daban-daban duk da cewa sun rubuta abubuwa masu amfani dangane da akidojin larabawan jahiliyya, amma abin dogaro da ya fi kowane daga ciki shi ne Kur’ani mai gima da yake magana a kan akidun larabawa a lokacin manzanci dangane da Allolinsu na gumaka, wanda sakamakon haka ne Kur’ani ya yaye mana sirrin da yake boye a cikin akidunsu na bautar gumaka. 
Wannan bangare na bincikemmu yana da gayar muhimmanci, saboda haka tare da amfani da ayoyin Kur’ani mai girma zamu yi bincike a kan dalilan da ya sa mushrikai suke bautar wanin Allah:
1-Izza Da Daukakar Mutanen Da Cin Nasararsu Wajen Yaki Duk Daga Gumaka Suke
Mushirikai lokacin manzanci sabanin masu tauhidi, sun yi imani da cewa daukaka da cin nasarar al’umma a wajen yaki duk yana zuwa ne daga gumaka kuma da taimakonsu ne zasu cimma hakan. Amma Kur’ani mai girma dangane da daukaka da cin nasarar masu kadaita Allah yana nuni da cewa:
A-Mai kadaita Allah yana samun daukaka ne daga Allah “Dukkan daukaka tana ga Allah”.
Amma shi kuwa mai bautar gunki yana ganin cewa daukaka da cin nasararsa tana zuwane daga Allah. Kamar yadda Kur’ani yake cewa: “Sun riki wanin Allah a matsayin abin bauta domin ya kasance dalilin daukakak a garesu”.
B-Mai tauhidi yana ganin dukkan cin nasararsa tana zuwa ne ga Allah kamar yadda wannan ayar take magane a a kai: “Babu ci nasara sai daga Allah wanda yake madaukaki mai hikima”
Amma wadanda suke mushrikai sun daukaka duk wani cin nasara yana zuwa ne daga Gumakansu da suka yi dakansu. Kamar yadda Kur’ani yake fadar cewa: “Sun riki wani Allah a matsayin abin bauta domin ko ya taimaka musu”. 
2-Wadanda Ceto Yake A Hannunsu
Mushirikai lokacin manzanci suna daukaka cewa gumakansu su ne ceto yake a hannunsu, sannan sun yi imani da cewa cetonsu ba tare da wani sharadi ba karbabbe ne, saboda haka muhimmi a nan shi ne kawai su bauta musu domin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kamar yadda ayar Kur’ani take cewa: “wane ne zai ceto a wajensa ba tare da izininsa ba”?. Ana iya samun wannan hakikar daga ma’anar wasu ayoyin .
3-Magudanar Ayyukan Ubangiji
Wannan akida ta daukar cewa ayyukan Allah sukan biyo ta hanyar gumaka ne, wani abu wanda yake da tsawon tarihi a cikin akidar bautar gumaka, ba wai ya takaita ne ba kawai ga mushirikai lokacin manzanci, domin kuwa tattaunawar Annabi Ibrahim da mushirikai lokacinsa ya tabbatar mana da wannan, domin kuwa ya kasance yana siffanta Ubangijinsa da hakan: “Shi ne wanda ya halicce ni kuma yake shiryar da ni. Sannan shi ne wanda yake ciyar da ni yake kuma shayar da ni. Sannan idan na yi rashin lafiya shi ne yake warkar da ni. Sannan shi ne yake kasha ni kuma yake raya ni, sannan shi ne nake tsammanin zai gafarta ma ni kurakuraina”.  A cikin wadannan ayoyin Annabi Ibrahim (a.s) wanda kuma yake shi ne gwarzon tauhidi. Yana nuni da cewa ayyuka makamantan Shiryarwa, azirtawa, ceto, kisa da rayarwa da gafarta zunubbai duk ayyuka ne na Allah madaukaki guda daya. Ta wannan hanyar ne kuma ya yi raddi a kan akidun mushirikai “Babil wadanda suka dauki sabanin hakan cewa duk suna zuwa ne daga gumaka.
4-Kishiyoyin Allah
Ayoyin da zasu zo nan gaba kadan suna bayyanar da yadda akidojin mushrikai suke ta yadda suke riya cewa wadannan gumaka nasu kishiyoyin Ubangiji ne:
A-”Akwai wasu daga cikin mutane wadanda suke daukar wasu sabanin Allah a matsayin kishiyoyi gareshi, sannan suna son su kamar son Allah”
Abin da ake nufi da kishiya kuwa shi ne, ta yadda suke daukar su abu guda wajen tafiyar da ayyukan da mu muke jibinta su zuwa ga Ubangiji, kamar yadda muka sani kashewa da rayawa da arzitawa da warkar da marar lafiya da yin gafara duk ayyuka ne na Ubangiji kuma wani reshe ne na rububiyyar Ubangiji wajen tafiyar da duniya. Amma masu bautar gumaka sun dauka duk wadannan ayyuka suna zuwa ne daga gumamakansu. kuma sakamakon haka ne suke bauta da yabo a garesu.
B-”Wallahi mun kasance muna cikin bata a bayyana ne. Yayin da muke daidaita ku da ubangijin duniya” .
 Tare da kula da ma’anonin wadannan ayoyin muna iya gane hakikain dalilin da yasa mushrikai suke bautar gumaka, saboda haka a nan zamu yi bincike ne a kan sakamakon da muka samu a cikin bahsinmu da ya gabata.
Sakamakon Da Zamu Iya Dauka Daga Bahsin Da Ya Gabata
1-Mushirikai a lokacin manzancin Manzo (s.a.w) da wadanda suka gabace shi duk sun yi imani da alloli kanana kuma wasu daga cikin ayyukan Ubangiji suna jibinta su zuwa ga wadannan allolin na su, duk da cewa suma abin halitta ne amma nauyin tafiyar da wasu ayyukan yana kansu. Wato suna da wani nau’i na rububiyyar Ubangiji, sakamakon haka ne suke bauta musu.
Sannan wannan ikon da gumaka suke da shi a kan duniya ba shi da wata iyaka, domin kuwa wani lokacin sukan jibinta wasu daga cikin ayyukan Ubangiji zuwa garesu. Kamar abin da ya hada da ruwan sama, ceto, warkar da marasa lafiya, da gafarar zunubbai, mushirikai lokacin manzanci sun kasance suna da wannan akida.
Ibn Hisham yana cewa: “Farkon wanda ya shigar da bautar gumaka a garin Makka da kewayanta shi ne Amru Bn Luhay, shi ne yayin dawowarsa daga tafiyar da ya yi zuwa Sham a wani yanki wanda ake kira da (Bulka) yayin da ya ga wadansu mutane suna cikin bautar gumaka, sai ya tambaye su sirrin wannan bauta, sai suka amsa masa da cewa. Wadannan gumaka da muke bauta su ne, suke saukar da ruwan sama, sannan muna neman cin nasara daga garesu. Sai Amru Bn Luhay ya ce musu: Shin zaku ba ni wani gunki in kai yankinmu ta yadda zasu bauta masa? Ta haka ne suka amsa wa Amru abin da ya bukata daga garesu. Sai suka ba shi wani babban gunki mai suna (Hubal) ya tafi da shi zuwa garin Makka sai suka kuwa dora shi bisa ginin Ka’aba sannan suka kira mutane zuwa ga bautarsa. 
2-Wani yana iya yin tunanin cewa nazarin mushrikai a kan gumaka bai wuce abin da ya shafi neman ceto ba ta hanayarsu zuwa wajen Allah, amma abin ba haka yake ba, domin kuwa ya saba wa ayoyin da muka ambata a baya. Domin kuwa ayoyin da suka gabata suna cewa mushrikai sun dauka cewa ceto, azurtawa da gafara, cin nasara da samun kariya duk yana zuwa ne daga gumakan da suka sassaka da hannuwansu, wato wani bangare ne na ayyukan Ubangiji sun jibinta shi zuwa ga gumakan.
Imani da cewa ceton gumaka daga Allah karbabbe ne duk da cewa kuskure ne, amma ba wani matsayi ba ne wanda zai sanya su dauke su matsayin kishiyoyi ga Allah, zuwa inda mushrikai a ranar kiyama zasu yi nadama a kan ayyukansu yayin da zasu ce: “lokacin da muke daidaita ku da ubangijin halitta”.
3-Manufar mushrikai dangane da bautar gumaka ya samo asali daga imanin da suke da shi a zukatansu a kan cewa wadannan gumaka su ne suke tafiyar da al’amuran duniya. Da wannan tunanin ne nasu suke bauta wa gumakan ta yadda suka dauke su a matsayin alloli kuma masu tafiyar da duniya, kuma masu ceto da shiryarwa.
4-Tare da kula da abin da muka ambata a baya muna fahimtar hakikanin ma’anar ibada ta yadda zamu iya bayyana ma’anar ibada da cewa: Ibada ita ce kaskantar da kai da girmamawa wanda ya samo asali ne daga akidar da suke da ita dangane da abin da suke bauta, wannan abin bautar kuwa Allah ne ko kuwa abin halitta (ta yadda a akidar mai bautar) wannan abin bautar yana tafiyar da ayyukan Ubangiji ne.
Da wani bayanin kuwa, Ibada ita ce kaskantar da kai da girmamawa ga abin da mutum ya dauka cewa shi ne Allah abin bauta, wannan kuwa ya kasance rububiyyarsa gaskiya ko ba gaskiya ba ce.
Imam Khomaini yana bayyana ibada da cewa: Ibada ita ce mutum ya dauki wani abu yana yabonsa a matsayin abin bauta, wannan abin kuwa a matsayin Allah babba yake ko kuwa Allah karami .
Duk wani nau’i na tawalu’u da girmamawa idan dai ba tare da wannan nufin a ka yi shi ba to ba ibada ba ne. Duk kuwa yadda ya kai matukar girmamawa da kaskantar da kai. Saboda haka kaskantar da kai daga masoyi zuwa ga abin da yake so, girmamawar da ga iyayensa, da girmamawar da muminai suke wa annabawa da waliyyai sam ba ya taba zama ibada. Saboda haka kowane daya daga cikin wadannan abubuwa yana da sunansa namusamman da ya kebanta da shi, wanda duka suna iya shiga karkashin girmamawa.
Maziyarta dakin Allah sukan sanya hannunsu su shafi bakin dutse (hajrul aswad) sannan sukan sumbaci dakin ka’aba sukan aza fuskarsu bisa bangon ka’aba suna yin kuka, sannan babu wani wanda yake ganin suna bautar yumbu da kasar da aka yi dakin ka’aba, domin kuwa ba su ganin cewa al’amarin tafiyar da duniya yana hannunsu (rububiyya) ta yadda zai zama suna bautarsu.
Saboda haka bahasimmu a kan Ma’anar ibada ya kawo karshe, yanzu mun samu damar da zamu iya yin magana a kan bidi’a sannan mu yi magana a kan iyakokinta, domin kuwa Bahasi a kan wadannan abubuwa guda biyu yana matsayin mabudi wanda zamu yi amfani da shi a bahsoshinmu na gaba.