Sakon Hakkoki




Sak'on Hak'k'ok'i
(Risalatul Huk'uk')

Na:
Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s)

Tarjamar:
Hafiz Muhammad Sa'id
 

 

Cibiyar Al'adun Musulunci ta buga Littafin da Yad'awa
00989193544585 - 002348028403359
ISBN: 964-7959-04-3

Littafin: Sak'on Hak'k'ok'i (Risalatul Huk'uk')
Na: Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s)
Tarjamar::   Hafiz Muhammad Sa'id
Mai Yad'awa:  Cibiyar Al'adun Musulunci
Bugu Na Farko:   1433, 20012, 1391
Gurin Bugawa:  Kano
Adadi:   10000
Email:    hfazah@yahoo.com
 
Da Sunan Allah Mad'aukaki
Godiya ta tabbata ga Allah (s.w.t)
Aminci ya k'ara tabbata ga bayinsa wad'anda ya zab'a
"Kawai Allah yana son ya tafiyar da daud'a daga gareku ne Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa " .
"Lallai ni mai bar muku nauyaya biyu ne; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku tab'a b'ata ba bayana har abada matuk'ar kun yi rik'o da su " .
Kuma sama ya d'aukaka ta, kuma ya sanya sikeli. Kuma ku daidaita awo da adalci, kada ku rage sikelin. Kuma k'asa ya sanya ta domin talikai ne .
 
Gabatarwa
Kamalar dan Adam wani abu ne mai wahalar isa zuwa gareshi domin hanyoyin suna da surkukiya mai wahalar gaske, sai dai akwai ma'aunai da suke nuna cewa mutum yana samun ci gaba. Wadannan ma'aunan suna iya kasancewa na tunani ko na aiki, ta yadda kyawawan halayen mutum su ne suke iya nuna cewa shi salihi ne ko fasidi ba yawan ibadojinsa ba, sau da yawa wani yake bauta amma babu inda take zuwa, imma dai don bai riki imamin zamaninsa ba, ko ya riki masoya Allah makiya, ko halayensa sun munana, don haka a cikin kyawawan halaye ne masu rige zasu yi rige domin kai wa ga kamala.
A cikin littafin alKafi na sheikh Kulaini ya zo daga gareshi daga Usman dan Isa, daga Ishak dan Ammar da waninsu, daga Abu Abdullah Imam Ja'afar Sadik (a.s) ya ce: Kada ku rudu da sallarsu, ko da azuminsu, domin sau da yawa ta yiwu mutum ya riki yin salla da azumi ta yadda da ya bar su sai ya samu jin babu dadi, amma ku jarraba su gun gaskiyar magana, da bayar da amana .
A wata ruwayar Imam Ja'afar Sadik yana cewa ne: Duk wanda harshensa ya gaskata, to aikinsa zai tsarkaka .
 Lamarin kiyaye hakkin mutane ya kai ga hatta cikin abin da ya shafi mutum ya hau kansa ya kiyaye hakkin mutane a cikinsa. Lamarin ya kai ga manzon Allah (s.a.w) yana la'anar mai cin guzurinsa (a tafiya) shi kadai ya bar sauran mutane.
Jarabawar da take gaban mutum tana da girma da wahala matuka, kuma kowacce ana son ya kiyaye cikinta don ya kasance mutum mai kamala wurin Allah madaukaki. Muna iya duba wannan ruwaya don muga santsin wannan hanya kamar haka:
Daga littafin Ihtijaj na Dabarasi, Mansur Ahmad dan Abi Dalib Addabrasi , da sanadinsa zuwa Imam Hasan al'Askari (a.s) daga Imam Ridha (a.s) ya ce: Aliyyu dan Husain (a.s) ya ce:
(Yaudara da nuna Salihanci) Idan kuka ga mutum yanayinsa da basirarsa sun kyautata, yana kaikaice maganarsa, da nuna kaskantar da motsinsa, to ku yi a hankali kada ya rude ku, sau da yawa a kan samu wanda samun duniya da hawa kan haram yake yi masa wahala saboda raunin niyyarsa, da wulakantuwarsa da tsoron zuciyarsa, sai ya nuna addini a matsayin tarkonsa, shi ba ya gushewa yana yaudarar mutane da zahirinsa, idan kuma ya samu damar aikata yin haram sai ya fada masa.
(Dukiya da Mata) Idan kuwa kuka same shi yana kamewa daga haram to (har yanzu dai) ku yi a hankali kada ya rude ku, domin lallai sha'awowin halittu suna sassabawa, sau da yawa wani wanda yake nisantar dukiyar haram komai yawanta, (amma) kuma (da zai samu dama, da) ya dora kansa (ya hau) kan wata mummunar mata mai muni (duk muninta) sai ya aikata haram (na zina) tare da ita.
(Samuwar Hankali) Idan kuwa kuka same shi yana kamewa daga wannan (zina) to (har yanzu dai) ku yi hankali da shi kada ya yaudare ku har sai kun duba hankalinsa, sau da yawa wani ya bar wannan duka amma ba shi da wani hankali mai karfi, sai ya kasance abin da yake batawa da jahilcinsa ya fi abin da yake gyarawa da hankalinsa.
(Son Zuciya) Amma idan kuka sami hankalinsa mai karfi ne, to (har yanzu dai ku yi hattara da shi) ku yi hattara dai kada ya yaudare ku har sai kun ga shin yana tare da son ransa a kan (watsi da) hankalinsa, ko kuma yana tare da hankalinsa ne a kan (watsi da) son ransa.
(Son Shugabanci Batacce) Sannan yaya sonsa yake ga shugabanci na barna da nisantarsa gareshi. Hakika a cikin mutane akwai wanda ya rasa duniya da lahira, yana barin duniya don duniya, yana ganin dadin jagorancin barna ya fi dadin dukiyoyi da ni'imar halal da aka halatta, sai ya bar wannan duka don neman jagoranci har sai idan aka gaya masa cewa ka ji tsoron Allah, sai girman kai ya kwashe shi da barna, to wutar jahannama ta wadatar masa, kuma tir da makoma .
Yana mai gangara kawararo gaba gadi, farkon barna tana jansa zuwa ga mafi nisan matukar tabewa, kuma ubangijinsa yana mai barinsa da kansa bayan nemansa ga abin da ba zai iya masa ba a cikin taurin kansa, shi yana mai halatta abin da Allah ya haramta, yana mai haramta abin da Allah ya halatta, ba ruwansa da abin da ya kubuce masa na addininsa idan dai shugabancin da ya tabe saboda shi ya kubuta, wadannan su ne wadanda Allah ya yi fushi da su ya la'ance su kuma ya tanadar musu da azaba mai wulakanci .
(Mutumin Kwarai) Sai dai cikakken mutum, madalla da mutumin da yake sanya son ransa kan biyayya ga umarnin Allah madaukaki, kuma karfinsa ya kasance ya bayar da shi cikin yardar Allah, yana ganin kaskanci tare da gaskiya shi ya fi kusanci zuwa ga daukakar har abada a kan daukaka cikin barna.
Kuma ya san cewa mafi karancin abin da zai iya jurewa na cutuwarta (duniya) zai kai shi ga dawwamar ni'ima ne a gidan da ba ya rasuwa ba ya karewa(lahira), kuma mafi yawan abin da yake samun sa na farin cikinta (duniya) idan ya bi son ransa zai kai shi ga azabar da babu yankewa gareshi babu gushewa (a lahira), to wannan mutumin madalla da shi (ya cika) mutum, da shi ne zaku yi riko, kuma ku yi koyi da sunnarsa (aikinsa), kuma ku yi tawassali da shi zuwa ga ubangijinku, domin shi ba a mayar masa da addu'a, kuma ba a hana shi abin da ya nema.
Littafin da yake gabanka mai karatu shi ne Littafin "Sakon Hakkoki" na Imam Aliyyu Zainul-abidin wanda aka san shi da asSajjad, ko "Sayyidus Sajidin". Shi bayani ne mai kima matuka da ya ishi mutun rayuwar duniya gaba daya, wanda da al'umma ta kiyaye shi, da ba a samu sabani tsakanin mutane biyu ba, da duniya ta koma kamar aljanna saboda zaman lafiya, da yalwa da arziki, da kauna da so sun maye gurbin kiyayya da gaba, da sulhu da zaman lafiya sun maye gurbin yaki da kashe-kashe!.
Imam Ali asSajjad shi ne Imami na Hudu cikin jerin wasiyyan annabi (s.a.w) wadanda su ne ruwayoyi suka ambace su da Ahlul-baiti da suka hada sayyida Zahara (s.a) da kuma goma sha biyu tsarkaka da manzon Allah (s.a.w) ya yi umarni da riko da su bayan wafatinsa kamar yadda ya zo a manyan littattafan ruwayoyi na hadisai. Sai dai kauce wa wannan wasiyya ta manzon Allah (s.a.w) ya sanya al'umma fadawa cikin rudani da bambance-bambance har zuwa wannan zamanin.
Allah (s.w.t) yana fada cewa: "Kawai Allah yana son ya tafiyar da daud'a daga gareku ne Ahlul-baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa" .
Wasiyyar manzon Allah (s.a.w) ga al'ummarsa: "Lallai ni mai bar muku nauyayan (alkawura) biyu ne; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su" .
Hadisai sun yi nuni da su a littattafai daban-daban, kamar yadda Shehu Usman dan Fodio Allah ya kara masa yarda ya kawo sunansu a cikin Nasihatu Ahluzzaman a yayin da yake kawo salsalar Imam Mahadi (a.s) wanda zai zo a karshen duniya. Da al'umma ta fuskanci koyarwarsu da ba ta samu kanta cikin wannan faganniya da rudani ba, sai dai abin da ya faru ya riga ya wakana.
Domin tubarraki zamu so kawo sunyensu kamar haka: Imam sayyidi Ali (a.s), sai Imam Hasan (a.s), sai Imam Husain (a.s), sai Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s) wanda shiryarwarsa take kunshe cikin wannan littafin, sai Imam Muhammad al'Bakir (a.s), sai Imam Ja'afar asSadik (a.s), sai Imam Musa alKazim (a.s), sai Imam Ali arRidha (a.s), sai Imam Muhammad al'Jawad (a.s), sai Imam Ali al'Hadi (a.s), sai Imam Hasan al'Askari (a.s), sai Imam Muhammad al'Mahadi (a.s).
Da yake ruwayoyi biyu ne, don haka mun kawo su da maimaicin da suka zo da shi a ruwayoyi mabambanta saboda sabanin da yake tsakaninsu, sai dai mun sanya ruwayar da tafi fa'idoji masu yawa, ita kuwa ruwayar da ta fi sanadi mai karfi mun sanya ta a kasa.
Muna rokon Allah ya sanya Imam Khoamain (k.s) cikin ladan wannan rubutun sakamakon yau ta yi daidai da ranar juyayin wafatinsa.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Islamic Cultural Foundation (Cibiyar Al'adun Musulunci)
Saturday, June 04, 2011
 
    Sakon Hakkoki
Na
Imam Aliyyu Zainul-abidin (a.s) dan Husain (a.s)

A wata ruwayar kuma an karbo ne kamar haka :
Ibn Musa ya karbo daga Al'asadi, daga alBarmaki, daga Abdullahi dan Ahmad, daga Isma'il dan alFadhal, daga Assumali, daga Sayyidul Abidin Aliyyu dan Husain (a.s) cewa ya ce: Hakkin ranka a kanka shi ne ka yi amfani da ita a biyayyar Allah mai grima da daukaka, kuma hakkin harshenka sai ka kare shi daga alfahasha har dai zuwa karshen ruwaya .
Ka sani Allah madaukaki yana da hakkoki da suka kewaye ka a cikin duk wani motsi da kake yi, ko wata nutsuwa da kake yi, ko wani hali da kake da shi, ko wani masauki da kake sauka, ko wata gaba da ka juya ta, ko wani abu da ka sarrafa.
Wasu hakkokin sun fi wasu girma, amma mafi girman hakkin Allah a kanka shi ne wanda ya wajabta maka ga kansa daga hakkinsa wanda shi ne asalin hakkoki daga gareshi ne suka yi rassa, sannan sai kuma abin da ya wajabta maka ga kanka tun daga samanka kanka har zuwa tafin kafarka, a bisa sassabawar gabobinka. Sai ya sanya wa ganinka wani hakki a kanka, ya sanya wa jinka wani hakki a kanka, ya sanya wa harshenka wani hakki a kanka, hannunka yana da wani hakki a kanka, kafarka tana da wani hakki a kanka, cikinka yana da wani hakki a kanka, farjinka yana da wani hakki a kanka, to wadannan su ne gabobi bakwai wadanda da su ne ake yin ayyuka.
Sannan sai madaukaki ya sanya wa ayyukan hakkoi a kanka, sai ya sanya wa sallarka tana da hakki a kanka, haka azuminka yana da hakki a kanka, sadakarka tana da hakki a kanka, kyautarka tana da hakki a kanka, kuma ayyukanka suna da hakkoki a kanka.
Sannan sai ya fitar da hakkoki a kanka zuwa ga waninka daga ma'abota hakkoki a kanka, sai ya wajabta su a kanka; hakkoki jagororinka, sannan sai hakkokin al'ummarka, sannan sai hakkokin danginka; wadannan su ne hakkokin da sauran hakkoki suke rassantuwa daga garesu.
To hakkokin jagororinka guda uku ne da ya wajabta su a kanka: hakkin mai jagorantarka da mulki, da hakkin mai jagorantakarka da ilimi, da hakkin mai jagorantakarka da mallaka, kuma duk mai jagorantarka shugaba ne.
Kuma hakkokin al'ummarka da ya wajbta a kanka guda uku ne: Hakkin al'ummarka da mulki, sai hakkin al'ummarka da ilimi domin jahili nauyin al'umma ne kan malami, sannan sai hakkin al'umma da mallaka kamar hakkin mata da abin da ka mallaka na kuyangi.
Kuma hakkokin dangi da aka wajabta a kanka suna da yawa daidai gwargwadon kusancin dangantaka: Hakkin babarka, sannan sai hakkin babanka, sai hakkin danka, sai hakkin dan'uwanka, sai hakkin nakusa, sai mai biye masa a kusanci, sai hakkin wanda ya fi cancanta, sai kuma mai biye masa.
Sannan sai hakkin ubangijinka mai ni'imta maka, sai hakkin ubangidanka wanda yake ni'imta maka, sannan sai hakkin masu kyautata maka, sai hakkin mai yi maka kiran salla, sai hakkin limaminka a sallarka, sai hakkin abokin zaman wuri daya, sai hakkin makocinka, sai hakkin abokinka, sai hakkin wanda kuka hada hannu, sai hakkin dukiyarka, sai hakkin wanda kake bin sa bashi, sai hakkin wanda yake bin ka bashi, sai hakkin wanda kuke cudanya da shi, sai hakkin wanda kuke gaba da rigima da ya kai ka kara kotu, sai hakkin wanda kuke gaba da rigima da ka kai shi kara kotu.
Sannan sai hakkin wanda ka nemi shawararsa, sai hakkin wanda yake ba ka shawara, sai hakkin wanda ya nemi ka yi masa nasiha, sai hakkin mai yi maka nasiha, sai hakkin wanda ya grime ka, sai hakkin wanda ka girma, sai hakkin mai tambayarka (rokonka), sai hakkin wanda ka tambaya (ka roka), sai hakkin wanda ya munana maka da wata magana ko wani aiki da gangan ne ya yi maka ko ba da gangan ba, sai kuma hakkin jama'arka a kanka, sai hakkin ma'abota zaman amana, sai kuma hakkokin da suke kanka daidai gwargwadon dalilan halaye, da sabuban da suka wakana.
To farin ciki yana ga wanda Allah ya taimaka masa a kan yin abin da ya wajabta masa na hakkokinsa, kuma ya datar da shi ga wannan, ya ba shi katari.
 
Hakkin Allah da Dan Adam
Hakkin Allah : "Amma hakkin Allah mafi girma, shi ne ka bauta masa, ba ka yi tarayya da shi da wani abu, idan ka yi haka da ihlasi, to Allah ya daukar maka alkawari a kansa cewa zai isar maka lamarin duniya da lahira, kuma ya kiyaye maka abin da kake so daga cikinsu".

Hakkin Rai :"Amma hakkin ranka a kanka shi ne ka sanya ta cikin biyayya ga Allah, sai ka ba wa harshenka hakkinsa, ka ba wa jinka hakkinsa, ka ba wa ganinka hakkinsa, ka ba wa hannunka hakkinsa, ka ba wa kafarka hakkinta, ka ba wa cikinka hakkinsa, sai ka ba farjinka hakkinsa, kuma sannan sai ka nemi taimakon Allah (s.w.t) a kan hakan.
Hakkin Harshe : "Kuma amma hakkin harshe; shi ne ka kare shi daga mummunar maganar alfahasha -da batsa-, da saba masa alheri, da barin maganar da ba ta da wani amfani, da kyautata wa mutane, da kyautata zance game da su, da siffanta shi da ladubba, da sanya masa takunkumi sai inda yake akwai bukata, da amfani ga duniya da addini, da kuma kame shi daga shiga dan zance mummuna mai karancin amfani, wanda ba kasafai ake kubuta daga sharrinsa ba, tare da karancin amfaninsa, kuma ya kasance bayan duban hankali a matsayin jagora a kansa, da yin adon mai hankali a cikin hankalinsa da doruwa bisa kyakkyawar dabi’arsa a cikin harshensa, sannan babu dubara babu karfi sai da Allah".
Hakkin Ji : "Amma hakkin ji shi ne a tsarkake shi game da kada ka sanya shi wata hanya zuwa ga zuciyarka sai da wata magana mai kima da zata haifar da wani alheri a cikin zuciyarka, ko ka samu wata kyakkyawar dabi'a, ka sani kofar magana zuwa ga zuciya tana kai wa ga haifar da ma'anoni kala-kala na abin da take kunsa na alheri ko sharri, kuma babu wani karfi sai da Allah".
Hakkin Gani :"Amma kuma hakkin gani shi ne ka rufe shi daga ganin abin da bai halatta ba, ka bar jefa shi (kana mai kallon ko'ina) sai wurin da yake abin lura ne, kana mai samun wata basira da shi, ko wani amfani na ilimi da shi, domin gani kofa ne na lura".
Hakkin Kafa : "Amma hakkin kafafuwanka, shi ne kada ka yi tafiya da su inda ba ya halatta gareka, kuma kada ka sanya takunka a hanyar da mutanenta ake wulakanta su, su (kafafuwa) masu daukarka ne su dora ka hanyar addini, sauran kokari kuwa ya rage maka, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Hannu : "Amma hakkin hannunka shi ne kada ka shimfida ta kan abin da bai halatta gareka ba, sai ka samu azabar Allah a gobe -kiyama- da wannan shimfidawar da ka yi, ka kuma samu zargi daga mutane a gidan yau -duniya-. Sannan kada ka rike shi daga abin da Allah ya wajabta mata, sai dai ka kiyaye shi da rike shi daga mafi yawan abin da bai halatta gareshi ba, da shimfida shi zuwa ga mafi yawan abin da bai zama wajibi a kansa ba, idan ya kasance ya hankalta, ya daukaka a wannan gida -duniya-, to lada kyakkyawa ya wajaba gareshi daga Allah a gidan gobe -lahira-".
Hakkin Ciki : "Kuma amma hakkin cikinka shi ne kada ka sanya shi salka -jaka- ga haram kadan ne ko mai yawa, kuma ka nufi halal da shi, kada ka fitar da shi daga haddin karfafa zuwa haddin wulakanci da zubar da mutunci, domin koshi mai kaiwa ne ga ma'abocinsa zuwa ga katon tumbi, mai sanya yin nawa da jinkiri, mai yankewa ne daga dukkan nagarta da karimci, kuma cika cikin da yake kai mai shi zuwa ga mayen koshi, mai sanya wulakanta kai da jahilci da zubar da mutunci ne".
Hakkin Farji : "Amma hakkin farjinka shi ne ka kare shi daga abin da bai halatta gareka ba, ka taimaka a kansa da rufe idanuwa, domin shi ne mafi taimakon abu, da kuma kiyaye shi da jin yunwa da kishirwa, da kuma yawaita ambaton mutuwa, da yin gargadi ga kanka saboda Allah, da tsoratar da ita da shi, kariya da taimako suna ga Allah ne, kuma babu dubara ko karfi sai da shi".
 
Sai kuma hakkokin ayyuka:
Hakkin Salla : "Kuma hakkin salla shi ne ka san cewa ita halartowa ce zuwa ga Allah madaukaki, idan ka san hakan, sai ka tsaya matsayin bawa mai kaskanci, mai kwadayi, mai tsoro, mai firgici, mai kauna, miskini, mai kaskan da kai, mai girmamawa ga wanda yake tsayawa gabansa da nutsuwa da rusunawa, da sunkuyar duk sasannin jikinsa, da tausasa gabobinsa, da kyautata ganawa da shi a kansa, da (neman) ya fansar maka da kanka wacce kurakuranka suka kewaye ta, kuma zunubanka suka halakar da ita, babu karfi sai da Allah.
Hakkin Salla: (Kuma hakkin salla shi ne ka san cewa ita halartowa ce zuwa ga Allah madaukaki, idan ka san hakan, sai ka tsaya matsayin bawa mai kaskanci, kaskantacce, mai kwadayi, mai tsoro, mai kauna, mai jin tsoro, miskini, mai kaskan da kai, ga wanda yake tsayawa gabansa da nutsuwa da dumanina. Ka fuskanto da zuciyarka a kanta, ka tsayar da haddodinta da iyakokinta, -tare da sunkuyawa da kaskan da gefe, da tausasa kafadu, da kyautata ganawa da Allah ga kansa, da kwadaituwa zuwa gareshi a kan fansar wuyanka wacce kurakuranka suka kewaye ta daga wuta, kuma zunubanka suka halakar da ita-).
Hakkin Azumi : "Kuma hakkin azumi shi ne ka san cewa shi wani hijabi ne da Allah ya sanya shi a kan harshenka da jinka, da ganinka, da farjinka, da cikinka, domin ya kare ka daga wuta da shi, idan ka sanya dukkan gabobinka cikin kariyarta sai ka kaunaci ka kasance abin karewa, amma idan ka bar su suna masu kaikawo cikin kariyarta, ka yaye suturar kariyar, sai ka hango abin da bai kamata ka gani ba na daga mai sanya maka sha'awa da karfin da ya fita daga cikin jin tsoron Allah, to fa ba ka da yakinin zaka iya yaga wannan kariyar (katangar da ka kutsa mata ka fada sabo) ka fita daga cikin (shi wannan sabon da ka fada masa), kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Sadaka : "Kuma hakkin sadaka (zakka) shi ne ka san cewa ita ajiyarka ce gun ubangijinka, kuma ajiyarka ce wacce ba ka bukatar sanya sheda a kanta, idan ka san haka sai ka kasance mafi amintuwa da abin da ka ajiye shi a sirrance fiye da abin da ka bayar da ajiyarsa a fili, kuma ka kasance ka cancanci zamantowa ka sirranta wani lamari gareshi ka shelanta shi, kuma lamari tsakaninka da shi ya zama sirri ta kowane hali ke nan, kuma sanya shedu da masu sanya idanu a kanta ba ya taimaka (maka) a kansa da wani abu, (idan ka yi haka) kamar ka fi nutsuwa ke nan a ranka, kuma kamar ba ka yarda da shi ba ke nan a kan bayar da ajiyarka wurinsa.
Sannan kada ka yi wa wani gori da ita domin taka ce, idan kuwa ka yi gori ga wani da ita, to ba ka amintuwa ka kasance kamar wulakanta kanka ne gareta gun wanda ka yi wa gorinta, domin wannan yana nuna cewa ba kanka kake nufi da ita ba, (ba ka yi wa kanka ajiya wurin Allah ba ke nan) domin da kanka kake nufi, da ba ka yi wa wani gori da ita ba, kuma babu wani karfi sai da Allah".
Hakkin Hadaya : "Amma hakkin hadaya shi ne ka tsarkake nufi zuwa ga Ubangijinka da ita, da kuma samun rahamarsa da karbuwarsa, kuma ba ka son idanuwan masu gani sai nasa kawai (don Allah kawai ka yi), idan ka kasance kamar haka ne, to ba ka kasance mai kallafa wa kai, ko mai dora wa kai ba, ka zama kawai Allah kake nufi. Ka sani Allah ana samun sa da saukakawa, ba a samun sa da tsanantawa. Kamar yadda ya so wa bayinsa saukakawa, ya ki musu tsanantawa.
Haka nan kaskantar da kai ya fiye maka daga kai, domin dora wa kai nauyi da wahalar da kai suna cikin halin masu tsaurin kai, amma kaskan da kai da rusanawa babu dora wa kai nauyi da wahalar da kai a cikinsu domin su ne asalin halitta, su samammu ne a cikin dabi'ar halitta. Babu karfi sai da Allah!
 
Sannan sai hakkokin Jagorori:
Hakkin Jagora : "Amma hakkin jagora shi ne ka san cewa shi jarrabawa ce gareka, kuma shi abin jarrabawa ne game da kai saboda abin da aka sanya a hannunsa a kanka na iko, kuma ka tsarkake masa nasiha, kada ka yi gogayya da shi, ka ga ke nan ka sanya shi ya sanya hannunsa a kanka sai ka kasance dalilin halakarka da halakarsa. Ka kaskan da kai da tausasawa domin ba shi yarda da kai da abin da zai kame shi daga gareka, kuma ba zai cutar da addininka ba, sai kuma ka nemi taimakon Allah a kansa a cikin dukkan wannan. Kuma kada ka yi masa takama ko ka yi gaba da shi, domin idan ka yi haka to sai ka sanya shi saba wa Allah da saba maka, sai ka sanya ranka ta fuskanci abin da kake ki, sai ka jefa shi halaka saboda kai (domin idan ya zalunce ka, zai fada halaka kuma kai ma zaka cutu), kuma kai ne ke nan ka zama mai taimaka masa a kanka, kuma mai tarayya da shi a abin da ya yi maka na mummuna (domin duk wanda ya taimaka wurin jagora ya yi masa ukuba, to ya yi tarayya da jagoran wurin cutar da kansa), kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Ilimi : "Kuma hakkin mai tarbiyyantar da kai da ilimi )mai ilmantar da kai) shi ne ka girmama shi, ka kuma karrama majalisinsa, da kyautata sauraronsa, da fuskantowa zuwa gareshi, da taimaka masa a kanka cikin abin da ba ka wadatuwa da shi na daga ilimi ta hanyar bayar da hankalinka, da halarto da fahimtarka, da tsarkake masa [zuciyarka] da bayyana masa ganinka ta hanyar barin jin dadi, da gudun sha'awa (domin idan ka zama nagari, to duk sa'adda ya gan ka zai ji dadin ganinka a matsayin yana da dalibi nagari), kuma ka san cewa duk abin da yake sanar da kai, sakonsa ne zuwa ga duk wanda ya hadu da kai daga jahilai, to sai ka lizimci kyakkyawar isarwa daga gareshi zuwa garesu, kada ka ha'ince shi wurin bayar da sakonsa, da kula da (isar da wannan sakon da ka samu) daga gareshi idan ka dauki nauyin yin hakan, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Ubangida: "Amma hakkin mai mulki da kai yana kama da mai mulki da kai a jagoranci, sai dai wannan -jagora- ba ya mallakar abin da wancan -mai bawa- yake mallaka. Don haka haka biyayyarsa ta zama wajibi a kanka a cikin komai karami da babba, sai dai idan wani abu ne da zai fitar da kai daga biyayyar hakkin Allah, wanda zai hana ka biyan hakkinsa (ubangiji) da hakkokin sauran halittu, idan ka gama da hakkinsa (ubangiji) sannan sai ka shagaltu da hakkinsa (ubangida), kuma babu karfi sai da Allah".
 
Hakkin Al'umma:
Hakkin Jama'a : "Amma hakkin jama'ar da kake jagoranta shi ne ka sani cewa sun zama jama'arka ce saboda karfinka a kansu, kuma ba komai ba ne ya sanya ka mahallin matsayin mai kula da su sai rauninsu da kaskantuwarsu. Babu wani abu da ya cancanci wanda rauninsa da kaskancinsa ya mayar da shi jama'arka, hukuncinka ya kasance mai zartuwa ne a kansa, ya kasance ba ya iya kare kansa daga gareka da wani karfi ko dubara, kuma ba ya iya samun mai taimako kan abin da ya fi karfinsa daga gareka sai Allah, in ban da ka yi masa tausayi da rahama da kariya da tausasawa. Kuma babu wani abu da ya fi cancanta gunka idan ka san abin da Allah ya ba ka na buwaya da karfi da ka yi rinjaye da shi, in ba ka kasance mai godiya ga Allah ba, wanda kuwa ya gode wa Allah, to zai ba shi wata baiwar abin da ya yi masa ni'imarsa da shi, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Ilimin Jama'a : "Amma hakkin jama'arka na ilimi shi ne; Ka san cewa Allah ya sanya ka mai kula da taskar abin da ya ba ka na ilimi, wanda ya jibinta maka shi na kula da taskar hikima, to idan ka kyautata cikin abin da ya ba ka na wannan kuma ka tsaya da shi a matsayin mai yi musu jiransa mai tausayi da nasiha irin na ubangida ga bawansa, mai hakuri mai neman lada, (kamar ubangida ne mai dukiyar bayi a hannunsa) wanda idan ya ga wata bukata sai ya biya masa ita daga dukiyar da take hannunsa, to (idan kai ma ka biya bukatun masu neman ilimi) ka kasance mai shiryarwa, kuma ka kasance abin buri da yarda. Idan kuwa ba haka ba, to sai ka zama mai ha'inci gareshi, kuma mai zalunci ga bayinsa, da keta huruminsa da na waninsa".
Hakkin Ilimin Jama'a: (Amma hakkin jama'arka na ilimi shi ne; Ka san cewa Allah ya sanya ka mai kula da taskar abin da ya ba ka na ilimi, wanda ya jibinta maka shi na kula da taskar hikima, to idan ka kyautata cikin abin da ya ba na wannan kuma ka tsaya da shi a matsayin mai yi musu jiransa mai tausayi da nasiha irin na ubangida ga bawansa, mai hakuri mai neman lada, (kamar ubangida ne mai dukiyar bayi hannunsa) wanda idan ya ga wata bukata sai ya biya masu ita daga dukiyar da take hannunsa, to (idan kai ma ka biya bukatun masu neman ilimi) ka kasance mai shiryarwa, kuma ka kasance abin buri da yarda. Idan kuwa ba haka ba, to sai ka zama mai ha'inci gareshi –Allah- kuma mai zalunci ga bayinsa, kuma ya hau kan Allah ya cire maka ilimi da kwarjininsa, ya shafe sonka daga zukata).
Hakkin Matar Aure : "Kuma hakkin wacce kake kula da ita da mallakar aure shi ne ka san cewa Allah ya sanya ta mazauni, wurin hutu, wurin nutsuwa gareka, da kariya, kuma haka nan ya wajabta wa kowannenku gode wa Allah game da samun abokin zamansa, ya san cewa wannan ni'ima ce tasa daga gareshi, kuma ya wajaba ya kyautata zaman ni'imar Allah ya girmama ta ya tausasa mata, duk da kuwa hakkinka a kanta ya fi karfi, biyayyarta gareka ta fi lizimtuwa cikin abin da ta so da wanda ta ki matukar ba sabo ba ne, sannan tana da hakkin tausayawa da debe kewa, da wurin zama gareta, biyan bukatar jin dadin da babu wakawa da ita, wannan kuwa abu ne mai girma, Babu karfi sai da Allah".
Hakkin Bawa : "Kuma hakkin wanda kake mallaka shi ne ka sani cewa shi halittar ubangijinka ne, kuma dan uwanka ne na uba da uwa, kuma tsokarka da jininka ne, ba ka mallake shi domin kai ne ka halicce shi ba Allah ba!, kuma ba ka halitta masa ji ko gani ba, ba ka gudanar masa da arzikinsa ba, sai dai Allah ne ya isar maka da dukkan wannan da wanda ya hore maka shi ya ba ka amanarsa, ya ba ka ajiyarsa, domin ka kare shi, ka yi masa halayen da Allah yake yi (wa bayinsa), sai ka ciyar da shi daga abin da kake ci, ka sanya masa abin da kake sanyawa, kada ka dora masa abin da ba zai iya ba, idan kuwa ka ki shi, to sai ka (mayar da lamarinka) zuwa Allah ka bar shi (ka rabu da shi), ka canja wani da shi, kada ka azabtar da halittar Allah, kuma babu karfi sai da Allah".
 
Hakkin Makusanta:
Hakkin Uwa : "Ka sani hakkin babarka cewa ita ta dauki cikinka a inda babu wani mutum mai iya daukar wani, ta ciyar da kai daga cikin zuciyarta da abin da babu wani mutum mai ciyar da irinsa ga wani, ta zama lokacinka da jinta da ganinta, hannunta da kafarta, gashinta da fuskarta, da dukkan gabobinta, tana mai murna da farin ciki, tana mai jure duk wani abin kinta, da zoginta, da nauyinta, da bakin cikinta, har dai hannun kudura ya cire ka daga gareta, kuma ta fitar da kai zuwa duniya, sai ta yarda da koshinka ita ta ji yunwa, ta tufatar da kai ita kuwa ta tsaraita, ta kosar da kai ita kuwa ta yi kishi, ta sanya ka inuwa ita kuwa ta sha rana, ta ni'imantar da kai da wahalarta, da jiyar da kai dadin bacci da rashin baccinta, cikinta ya kasance wurin zama gareka, dakinta ya zamanto matattara gareka, kuma nononta ya zama salkar sha gunka, ranta kuma kariya ne gareka, tana shan zafin duniya da sanyinta don kare ka, to sai ka gode mata a kan wannan sai dai ba zaka iya ba sai da taimakon Allah da dacewarsa".
Hakkin Uba : "Kuma hakkin babanka ka sani shi ne asalinka kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan, babu karfi sai da Allah".
Hakkin Da : "Kuma hakkin danka shi ne ka san cewa shi daga gareka yake kuma abin rabawa zuwa gareka a wannan duniya da alherinsa da sharrinsa, kuma kai abin tambaya ne kan abin da ka koya masa na kyakkyawan ladabi da shiryarwa ga ubangijinsa mai girma da buwaya, da kuma taimaka masa kan biyayyarsa ga Allah game da kai da kanka, to kai abin ba wa lada ne kan hakan kuma abin yi wa ukuba (idan ka cutar da shi ko ka yi sakacin tarbiyyarsa). To sai ka yi aiki cikin umarninsa irin aikin mai kawata aikinsa ta hanyar kyautata tarbiyyarsa tun a nan duniya, aikin mai yanke uzuri wurin ubangijinsa da abin da yake tsakaninsa da shi ta hanyar kyautata kula da shi da karba masa daga gareshi, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Dan'uwa : "Kuma hakkin dan'uwanka shi ne ka sani cewa shi ne hannunka da kake shimfidawa, kuma bayanka da kake jingina da shi, kuma daukakarka da kake dogaro da ita, kuma karfinka da kake ijewa da shi, don haka kada ka rike shi makami a kan sabon Allah, ko ka sanya shi tanadi domin zaluntar halittar Allah, kuma kada ka bar taimakonsa da agaza masa kan makiyinsa, da shiga tsakaninsa da shaidancinsa, da ba shi nasiha, da fuskantuwa zuwa gareshi a tafarkin Allah, to idan ya karkatu zuwa ga ubangijinsa, (Ubangijin) ya kyautata amsa masa, in kuwa ba haka ba, to Allah ya kasance shi ne ya fi zabuwa gunka, kuma mafi girma gareka fiye da shi".
Hakkin Mai 'Yantawa : "Amma hakkin mai 'yanta ka, mai ni'imata maka, shi ne ka sani cewa ya ciyar da dukiyarsa kanka, ya fitar da kai daga kaskancin bauta da dimuwarsa zuwa ga izzar 'yanci da nutsuwarta, sai ya sake ka daga ribacewar mallaka, ya kwance ka daga kaidin bauta, ya fitar da kai daga gidan sarkar (bauta), ya samar maka da hutun izza, ya fitar da kai daga kurkukun rinjaya, ya kare maka tsanani, ya shimfida maka harshen adalci, ya halatta maka duniya dukkanta, ya mallaka maka kanka, ya kwance maka daurin ribacewa, ya ba ka damar bautar ubangijinka, ya jurewa tawayar dukiyarsa da wannan, to ka sani shi ne mafi cancantar halitta da kai bayan danginka na jini a rayuwarka da mutuwarka, kuma shi ya fi cancantar kowa da taimakonka da agajinka, da kariyarka a tafarkin Allah, don haka kada ka taba zabar kanka a kansa har abada matukar yana bukatar ka".
Hakkin 'Yantacce : "Amma hakkin wanda ka 'yanta shi wanda ni’imarka take kansa, shi ne ka sani cewa Allah madaukaki ya sanya ka mai kariya gareshi, mai garkuwa mai taimako mai dabaibayi gareshi, kuma ya sanya ka tsani da sababi tsakaninka da shi, to shi ya cancanci zama kariyarka daga wuta, sai ladanka saboda shi ya kasance daga gareshi a lahira, a duniya kuwa ya ba ka gadonsa idan ba shi da dangi na jini, sakamakon abin da ka ciyar na dukiyarka (a kansa), ka tsayu da shi na hakkinsa bayan ciyar da dukiyarka, idan kuwa ba ka tsayu da kula da hakkinsa ba, to ana jiye maka tsoron kada gadonsa ya yi maka dadi, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mai Yin Alheri : "Amma hakkin wanda ya yi maka alheri shi ne ka gode masa, ka kuma ambace shi da alheri, ka samar masa da maganar (mutane) ta alheri (a kansa), ka tsarkake yi masa addu'a a tsakaninka da Allah mai girma da buwaya. Idan ka yi haka zai zama ka gode masa a boye da a sarari, sannan idan ka samu dama wata rana kai ma ka rama masa (alherin da ya yi maka), idan kuwa ba haka ba, to sai ka saurari damar da zaka (rama masa) kana mai sanya wa ranka wannan".
Hakkin Ladani : "Amma hakkim mai kiran sallah shi ne ka sani cewa shi mai tuna maka ubangijinka mai girma da daukaka ne, kuma mai kiran ka zuwa ga rabautarka, mafi girman mai taimakonka kan sauke wajibin Allah da yake kanka, sai ka gode masa a kan haka irin godiyar da kake yi wa masu kyautatawa. Idan kuwa ka kasance mai muhimmantar da gidanka ne (ta yadda ko ya yi kiran sai ka yi zamanka), to kai ba ka muhimmantar da lamarinsa na Allah ba, ka sani shi ni’imar Allah ce kanka babu kokwanto cikinta, to ka kyautata kasancewa tare da ita da godiyar Allah kanta a kowane hali, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Limami : "Amma hakkin limaminka a sallarka, shi ne ka sani cewa kai kana dora masa nauyin jakadancin tsakaninka da ubangijinka mai girma da buwaya ne, ya yi magana maimakonka kai ba ka yi magana mai makonsa ba, ya yi maka addu'a kai ba ka yi addu'a gareshi ba, kuma ya isar maka da tsoron tsayuwa gaban Allah mai girma da daukaka da yi maka rokonsa kai ba ka isar masa da wannan ba. Idan an samu wata tawaya tana kansa ban da kai, idan ya kasance mai sabo ne to kai ba ka yi tarayya da shi a cikinsa ba, kuma ba shi da wani fifiko a kanka (cikin alherin da ake samu), sai ya kare maka kanka da kansa, sallarka da sallarsa, to sai ka gode masa a kan hakan, kuma babu karfi da dubara sai da Allah".
Hakkin Abokin Zama : "Amma hakkin abokin zamanka sai ka tausasa masa dabi'arka, ka yi masa adalci a yin magana, kada ka kura masa idanuwa yayin da kake kallo, kuma ka yi nufin fahimtar da shi idan ka yi magana, idan kai ne ka zo wurin zamansa to kana da zabin tashi idan ka so, idan kuwa shi ne ya zo wurin zama gunka yana da zabi ya tashi amma kai ba ka da zabin tashi ka bar shi sai da izininsa, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Makoci : "Amma hakkin makocinka shi ne ka kiyaye shi idan ba ya nan, ka girmama shi idan yana nan, ka taimaka masa ka agaza masa a duka halayen biyu, kada ka bibiyi sirrinsa, kuma kada ka binciki wani mummunan abu nasa da ka sani, idan kuwa ka sani ba tare da ka bincika ba ko ka dora wa kanka neman sanin, to sai ka zama mai matukar katangewa mai matukar suturtawa, ta yadda da masuna zasu nemi kaiwa ga wani sirrin da ba su iya kaiwa ba saboda tsananin tattarewa gareshi, kada ka saurare shi (da satar jin me yake cewa) ta yadda bai sani ba. Kada ka sallama shi yayin tsanani, kada ka yi masa hassada yayin wata ni’ima, ka yafe masa kurakuransa, ka yafe masa laifinsa, kada ka bar yin hakuri da shi yayin da ya yi maka wauta, kuma kada ka fasa zama mai aminci gareshi, kada ka yi masa raddin zagi, ka kuma bata makircin mai zuwa (da sunan yi maka) nasiha (kansa), ka zauna da shi zaman mutunci, kuma babu dubara babu karfi sai da Allah".
Hakkin Aboki : "Amma hakkin aboki shi ne ka yi abota shi da fifita (shi) matukar ka samu damar yin hakan, idan kuwa ba ka yi ba to mafi karanci shi ne ka yi masa adalci, ka girmama shi kamar yadda yake girmama ka, ka kiyaye shi kamar yadda yake kiyaye ka, a tsakaninka da shi kada ka bar shi ya riga (ka) gaggawa zuwa ga wani alheri, idan kuwa ya riga (ka yin alheri) to sai ka saka masa, kada ka takaita masa abin da ya cancanta na kauna, ka dora wa kanka yi masa nasiha, da nuna masa hanya, da dora shi kan biyayyar ubangijinsa, da taimakonsa ga kare kansa cikin abin da ya yi nufi na sabon ubangijinsa, sannan ka kasance rahama gareshi, kada ka zama masa azaba, kuma babu karfi sai da Allah.".
Hakkin Abokin Tarayya : "Amma hakkin abokin tarayya (wanda kuka hada hannun cinikayya) shi ne idan ba ya nan sai ka kare shi, idan yana nan sai ka daidaita kanka da shi, kada ka yi wani hukunci sai da nasa hukuncin, kada ka yi aiki da ra'ayinka ba tare da tasa mahangar ba, ka kiyaye masa dukiyarsa, kada ka ha'ince shi cikin abin da yake babba ne ko karami, ka sani labari (daga manzon Allah) ya isar mana cewa; hannun Allah yana tare da hannayen masu tarayyar (hada hannun jari) matukar ba su ha'inci juna ba, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Dukiya : "Amma hakkin dukiyarka shi ne kada ka dauke ta sai ta hanyar halal dinta, kada ka ciyar da ita sai ta halal, kada ka karkatar da ita daga inda ta dace, kada ka juyar da ita daga hakkinta, kuma kada ka sanya ta ko’ina idan dai daga Allah take sai gareshi tsani zuwa gareshi, kada ka zabi kanka da ita a kan wanda tayiwu ba ya gode maka, ta yiwu (mai gadonka) ba zai kyautata gadon abin da ka bari ba, tayiwu ba zai yi biyayyar Allah da ita (dukiyar) ba sai ya zama kai ka taimaka masa a kan hakan, ko kuma ya zama ya kyautata gani ga kansa da abin da ya farar a dukiyarka sai ya yi biyayya ga Allah da ita, sai ya tafi da riba (ladan aikin alheri da ita) kai kuma ka koma (lahira) da zunubi (saboda tarin haram da ka yi) da hasara da nadama tare da tababbun (mutane), kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mai bin Bashi : "Amma hakkin mai bin ka bashi da yake neman ka biya, to idan kana da yalwa sai ka ba shi, ka isar masa da ita ka wadata shi, kada ka hana shi ka yi taurin bashi. Domn Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “Taurin bashin mawadaci zalunci ne”. Idan ka kasance maras yalwa, to sai ka nemi yardar da shi da kyautata magana, ka nemi (ya sake ba ka dama ta hanyar) kyakkyawan nema, ka mayar da shi daga kanka mayarwa mai taushin (hali), kada ka hada masa (zafi biyu na) karbar dukiyarsa da yi masa mummunar mu’amala, wannan wani mummunan hali ne, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Abokin Cudanya : "Amma hakkin Abokin cudanya shi ne kada ka yi masa 'yar rufe, kada ka yi masa zambo, kada ka yi masa karya, kada ka shammace shi, kada ka yi masa yaudara, kada ka yi wai abu na muzantawa gareshi irin aikin makiyin da ba ya rage wa abokinsa komai, idan kuwa ya samu nutsuwa da kai sai ka raga masa ga kanka, ka sani cewa yaudarar wanda ya sakankance (ya saki jiki) da kai (daidai yake da zunubin) cin riba, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mai Kara : "Amma hakkin abokin shari'a wanda ya yi da'awar wani abu a kanka, shi ne idan abin da yake da'awarsa a kanka gaskiya ne to kada ka bata hujjarsa, kuma kada ka yi kokarin lalata da’awarsa, sai ka yi husuma da kanka saboda shi, ka yi hukunci a kanka, ka yi sheda gareshi a kanka da hakkinsa ba tare da shedar shedu ba. Amma idan abin da ya yi da'awarsa a kanka ya kasance karya ne, to sai ka tausasa masa, ka hada shi da (girman) addininsa, ka karya zafafawarsa gareka da ambaton Allah. (Ka sani) Jefa masa batanci da mummunar magana ba ya iya kawar maka gabar makiyinka, (idan ka bace shi) sai dai kawai ka samu zunubinsa, da wannan ne kuma zai sake wasa takobin gaba da kai, domin batanci yana tayar da sharri ne, alheri kuwa yana gamawa da sharri ne, kuma babu dubara sai da Allah".
Hakkin Wanda ake Kara : "Amma hakkin abokin shari'a da ka kai shi kara, (ka sani) idan ka kasance mai gaskiya a kararka to sai ka kyautata maganarsa da (neman) hanyar (samun) mafitar karar, domin kara tana da zafi a cikin jin wanda ake kaiwa kara, kuma ka yi nufin hujjarka da tausasawa, ka saurara kadan, sai ka yi bayani dalla-dalla, ka tausaya da tausayi, kada jayayya da shi da ance-ance ta shagaltar da kai ga barin hujjarka, sai hujjarka ta tafi, kuma ya zama ke nan ba ka da wata riba a nan, kuma babu karfi sai da Allah ".
Hakkin Mai neman Shawara : "Amma hakkin mai neman shawara shi ne; idan wata makamar ra’ayi ta zo maka to sai ka ba shi nasihar, ka yi masa nuni da abin da ka san cewa da kai ne a matsayinsa da ka yi aiki da shi, ya kasance akwai rahama da tausasawa daga gareka, ka sani tausasawa tana kawar da dimuwa, amma kausasawa tana kawar da nutsuwa. Amma idan wani ra’ayi bai zo maka ba, kuma ka san wani wanda ka amintu da ra’ayinsa, ka yarda da shi ga kanka, to sai ka nuna masa shi ka shiryar da shi zuwa gareshi, sai ka zama ba ka hana shi wani alheri ba, ba ka boye masa nasiha ba, kuma babu dubara babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mai bayar da Shawara : "Amma hakkin mai ba ka shawara shi ne kada ka tuhume shi idan ya ba ka shawarar ra'ayinsa cikin abin da bai yi muwafaka da kai ba na ra'ayinsa, ka sani ra’ayoyi ne da yadda kowa yake gani da sabanin mutane, ka ba shi nasa zabin ra’ayi idan ka tuhumi ra’ayinsa, amma tuhumarsa ba ta halatta gareka idan dai shi ya kasance wanda yake cancantar neman shawararsa ne gunka, kuma kada ka bar yi masa godiya bisa abin da ya bayyana maka na ra’ayinsa, da kyakkyawar madafar shawararsa. Idan kuwa ya yi muwafaka da kai to sai ka gode wa Allah mai girma da daukaka, ka karbi wannan shawarar daga dan’uwanka da sauraron damar saka masa da irin wannan duk sa’adda ya zo maka da tasa neman shawarar, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mai neman Nasiha : "Amma hakkim mai neman nasiha shi ne ka ba shi nasihar gaskiya wacce kake ganin zai dauka, ka ba shi mafitar da zata tausasa a jinsa, ka yi masa maganar da hankalinsa zai dauka, ka sani kowane mai hankali yana da abin da zai iya dauka na magana da yake iya gane ta kuma ya karbe ta, kuma ma’auninka ya kasance shi ne tausayawa, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mai yin Nasiha : "Amma hakkin mai yin nasiha shi ne ka tausasa masa dabi'arka, ka rusuna masa zuciyarka, ka bude masa jinka (ka ba shi fuska), har sai ka fahimci nasiharsa, sannan sai ka yi duba cikinta, idan ya kasance ya dace cikinta sai ka gode wa Allah a kan haka, ka karba daga gareshi ka yi masa alherin nasiharsa. Amma idan kuwa tausayawarsa ba ta samu yin katari ba, kada ka tuhume shi, ka sani cewa shi bai yi maka rowar nasiha ba, sai dai kawai ya yi kuskure ne. Sai dai kuwa idan ya cancanci tuhuma ne a wurinka, to kada dai ka kula da komai nasa ta kowane hali, kuma babu dubara sai dai Allah".
Hakkin Babba : "Amma hakkin babba shi ne ka girmama shi saboda shekarunsa, da daukaka musuluncinsa idan ya kasance daga ma’abota falala a musulunci saboda rigonsa a cikinsa, da barin jayayya da shi gun husuma, kada ka riga shi wata hanya, kada ka shiga gabansa a wata hanya, kada ka nuna jahilcinsa, idan kuwa ya yi maka wauta to sai ka jure ka daure, ka girmama shi saboda hakkin musulunci da alfarmarsa da shekarunsa, ka sani hakkin shekaru da darajar (gwargwadon) musulunci ne, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Karami : "Amma hakkin karami shi ne ka tausaya masa, da wayar da shi, da koyar da shi, da yi masa afuwa, da suturta masa, da tausasa masa, da taimaka masa, da rufa masa asirin munanan da ya yi lokacin yarinta da kuruciya wannan shi ne (zai zama) dalilin tubansa da tausasa mu’amala da shi, da barin tsokano shi, domin wannan shi ne ya fi kusa da shiryuwarsa".
Hakkin Mai Roko : "Amma hakkin mai roko shi ne ka ba shi idan alamar gaskiyarsa ta bayyana, kuma (ya zama) kana da ikon biyan bukatarsa, da yi masa addu’ar (Allah ya yaye masa) abin da ya same shi (na talauci), da taimakonsa ga abin da yake neman sa, idan kuwa ka yi kokwanton gaskiyarsa (don haka sai) ka riga tuhumarsa ba ka yi masa wani alheri ba, to ba ka sani ba ko makircin shedan ne da yake son ya hana ka rabautarka ya kare maka kusanci da ubangijinka. Kuma ka bar shi cikin rufin asirinsa (kada ka tona shi idan ka san ba mabukaci ba ne), sai ka mayar da shi mayarwa kyakkyawa (wato kada ka kyare shi sai dai ka hana shi kawai ba tare da wani muzanta masa ba), amma idan ka rinjayi ranka cikin lamarinsa (ka ga ya kamata ka kyautata ka bar zatonka), sai ka ba shi abin da ya nema gunka, to wannan yana daga cikin manyan alherai".
Hakkin Wanda ake Roka : "Amma hakkin wanda ake roka shi ne idan ya bayar to sai ka karba daga gareshi da godiya gareshi, da sanin kyautatawarsa, ka nema masa uzurin hana ka (idan ya hana ka), ka kyautata masa zato, ka sani cewa idan ya hana dukiyarsa ya hana ke nan, kuma babu zargi a dukiyarsa, idan kuwa ya kasance mai zalunci ne (da hana ka), to mutum mai yawan zalunci ne mai yawan kafirci (rashin godiya)".
Hakkin Mai Farantawa : "Amma hakkin wanda Allah ya faranta maka rai ta hanyar sa (ta hannunsa), idan da gangan ne ya yi maka to sai ka gode wa Allah sannan sai ka gode masa a kan hakan da gwargwadonsa a mahallin sakamako, ka rama masa a kan kyautatawar farawa da ya yi, ka yi sauraron sai ka rama masa. Amma idan ba da gangan ne (ya faranta maka) ba, to sai ka gode wa Allah ka gode masa, ka sani cewa wannan ka samu ne daga gareshi (Allah) kai kadai, kuma ka so wannan lamarin idan ya kasance dalili ne na samun ni’imar Allah gareka, kuma (shi wannan mutumin) ka so masa (samun) alheri bayan wannan, domin dalilan ni’ima suna da albarka duk inda suke ko da ba na gangan ba, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mai Batawa : "Amma hakkin wanda aka kaddara samun mummuna (bacin rai) ta hannunsa da wata magana ne ko wani aiki, idan ya kasance da gangan ne to kai ka fi cancanta da ka yi afuwa, saboda abin da yake cikin (yin afuwar) na kunyata shi, da kyautatuwar ladabinsa, tare da wasu (mutanen) masu yawa irinsa na daga halittu (tayiwu su ma su dauki darasin). Domin Allah madaukaki yana cewa: “Duk wanda ya nemi taimako bayan zaluntarsa to wadannan babu wani laifi a kansu….. daga manyan alherai” (Shura: 40)".Da kuma fadinsa madaukaki: “Idan kuka yi (ramuwar wata) ukuba, sai ku yi ukuba da irin abin da aka yi muku ukuba da irinsa, amma idan kuka yi hakuri to wannan shi ne ya fi alheri ga masu hakuri” Nahal: 126. Wannan duk a cikin (munana maka) da gangan ke nan.
Amma idan bai zama da gangan ba, to kada ka zalunce shi da ganganta neman yin fansa kansa, sai ka kasance ka dauki fansa da gangan a kan abin da yake bisa kuskure ne, sai dai ka tausaya masa, ka mayar da shi da tausasawa yadda zaka iya, kuma babu karfi sai da Allah".
Hakkin Mutanen Gida : "Amma hakkin mutanen gidanka gaba daya shi ne ka sanya jin aminci, da yada tausayi, da tausasa wa mai sabawarsu, da yin sabo da su, da neman gyaransu, da godiya ga mai kyautatawarsu ga kansa da kuma gareka, domin (wanda ka) kyautata wa kansa shi ma (wannan aikin) kyautata maka ne idan ya kame cutarwarsa gareka, ya isar maka nauyinsa (ya wadatu da kansa), ya kame kansa daga (cutar) da kai. To ka game su gaba daya da addu’arka, da taimaka musu gaba daya da taimakonka, ka sanya su gaba daya a matsayinsu wurinka, babbansu a matsayin uba, karaminsu a matsayin da, matsakaicinsu a matsayin dan’uwa. Kuma duk wanda ya zo maka sai ka yi sabo da shi da tausasawa da tausayawa, ka sadar da zumuncin dan’uwanka da abin da yake wajibi ne kan dan’uwa a kan dan’uwansa.
Hakkin 'Yan Amana : "Amma hakkin 'yan amana (wadanda ba musulmi ba da suke rayuwa tare da musulmi bisa yarjejeniyar rayuwa tare), hukuncinsu shi ne ka karbi abin da Allah ya karba daga garesu (na su yi nasu addinin da rayuwarsu), ka cika musu abin da Allah ya sanya musu na nauyinsa da alkawarinsa, ka yi musu maganarsa cikin abin da suka nema ga kawukansu da aka tilasta su a kansa, ka yi hukunci garesu da abin da Allah ya yi hukunci da shi a kanka cikin abin da yake gudana tsakaninka da su a mu’amala.
Kuma kiyaye alkawarin Allah da cikawa da nauyinsa da ka dauka da nauyin alkawarin Manzon Allah (s.a.w) da ka dauka ya kasance maka katanga da zata hana ka zaluntarsu, domin labarin fadin Manzon Allah (s.a.w) ya isar mana cewa: “Duk wanda ya zalunci dan amana, to ni ne abokin husumarsa”. To ka ji tsoron Allah, kuma babu wata dubara ko karfi sai da Allah".
Wadannan su ne hakkoki hamsin da suka kewaye ka, ba ka iya fita daga cikinsu ta kowane hali, wajibi ne ka kiyaye su, da aiki da abin da suka kunsa, da taimakon Allah mai girman yabo a kan wannan, babu dubara babu karfi sai da Allah .
Godiya ta tabbata ga ubangijin talikai