Ra'ayoyin JagoranciMahangar Mutane game da Imamanci

MAHANGA BIYU KARKATATTU

Godiya tabatta ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah da alayesa da wadanda suka yi koyi da shiriyarsu.

Akwai karkatattun  dubi guda biyu kan al’amrin Imam Sadik (a.s) wadanda suka samo asali daga nau’i biyu na tunani. Abin mamaki a nan shi ne duk da sabawarsu da juna suna da kusaci wajen kamanni da abin da suka kunsa da kuma tushe, kai ana ma iya cewa wadannan dubi biyu suna da cikakkar tarayya a sashen ginshikansu.

MAHANGA TA FARKO:-

Ra’ayi ko kuma kallo irin na masu karewa watau masoya, wannan ra’ayin wasu masu zaton su mabiyan Imam Sadik (a.s) ne amma shi’arsa ne da fatar baki kawai banda aiki. Ra’ayin a takaice shi ne:-

Cewa Imam Sadik (a.s) ya sami yanayin da imaman da suka gabace shi ko suka biyo bayan shi basu samu ba, yanayin da ya ba shi damar yada hukunce-hukuncen addini da kuma bude wa dalibai kofofin majlisinsa. Ya zauna gidansa yana karbar masu zuwa, ya rungumi karantarwa da yada ilmomi, duk dalibi ko mai bidar gaskiyan da ya zake masa yana kashe kishinsa na ilmi. Mutum dubu hudu suka yi karatu a gabansa, kuma ta hanyar wadannan dalibai ilmomin Imam Sadik sun watsu a ko ina. Daga cikinsu akwai ilmomin addini kamar su fikihu da hadisi da tafsiri, akwai kuma ilmomin dan’adamtaka kamar su tarihi da kyawawan dabi’u da  ilmin zamantakewar al’umma.

Imamu ya yi mukabala da ma’abota sababbin ra’ayoyi, ya yi raddi kan zindikai da yan maddiyya da mulhidai, ko dai kai tsaye ko kuma ta hanyar dalibansa. Ya yi yaki da mazowa karkatattun addinai matuka. A ko wani fagen addini Imam ya tarbiyantar da wasu fitattun dalibai da kwararru.

Ma’abota wannan mahanga suna  karawa da cewa: domin burin Imam a kan ci gaban wannan gagarumin aikin ilmantarwa, dole ta sa ya guji sa baki cikin al’amuran siyasa, saboda haka bai gabatar da kowani aikin siyasa ba, bugu da kari ya ma zabi hanyar daidaitawa da irin siyasar halifofin zamaninsa domin dadada musu da nisantar duk wata rikitarwa da ka iya kusantar aikinsa. Don haka bai yi fito-na-fito da halifofin ba, ya kuma hana kowa yin hakan. Wani zubin ma yanayi yana sawa Imam ya je gaisuwa ya kuma sami kyaututtuka da goyon bayansu. Idan  shugaba ya yi masa mummunan zato sakamakon faruwar wata harkar tawaye ko kuma tsegunta masa wata tuhuma, Imam ya kan  je gaban shugaban domin ba da baki.

Ma’abotan wannan dubin su kan jero hujjojin tarihi domin karfafa ra’ayinsu. Hujjojin sun hada da riwayar Rabi’u Alhajib da makamantansa,

7  wadanda suke siffanta Imam da baiyana kuskure da nadamarsa a gaban Halifa Mansur. Wannan riwaya tana dangantawa Imam kalmomin yabon Mansur, wanda ko shaka babu karya ce a ce sun fito daga Imam Sadik (a.s.) dangane da azzalumai irinsu Mansur. Wadannan kalmomin suna sifanta Mansur cewa kamar Yusuf da Sulaiman da Ayyuba ya ke, suna neman ya dauki hakuri kan munana masa da Imam ko ‘ya’yan Hassan suke masa:  “Hakika an baiwa Sulaiman (mulki) kuma ya yi godiya, an jarrabi Ayyuba, ya yi hakuri, kuma an zalunci Yusufu, ya yi  gafara, kai kuma irinsu ne……”[1]

Wannan ra’ayi yana sifanta Imam da cewa shi masani ne mai bincike, Abu Hanifa da malik sun sha daga kogin ilminsa, sai dai ya yi matukar nisantar yaki da zaluntar addini da masu mulki ke yi, ya kuma nisanci bukatun umurni da kyakkyawan aiki da hana munkari yayin da sarki ya zama ja’iri. Imam ba shi da wata dangantaka da masu tawaye wa zalunci ire-iren su Zaid ibn Ali da Muhammad bn Abdullah da Hassan bn Ali shahidin Fakh ko kuma rundunonin wadannan mutane. Bai kasance yana mai da martani kan abin da yake aukawa jama’ar musulmi, ko nuna damuwa kan dimbin dukiyar da Mansur yake tarawa, ko yunwar da ‘ya’yan Annabi (s.a.w.a) suke fama da ita a cikin tsaunukan Tabaristan da Mazandaran da garuruwan Irak da Iran ba, ta yanda basu da abinda zasu sa a baka ko abinda zai rufe musu al’aura idan suna son  salla a jam’i  !! Kuma ba ruwansa da kisa da azabtarwa da tarwatsa mabiyansa alhali suna hannu rabbana basu samun ko da kwatankwancin abin da marasa galihun wancan lokaci suke mora!!!1 2 3 4 next