Ma'anar Shi'anciMa'anar Shi'anci a gurin Ahlul Bait (A.S.)

Imaman Ahlul Bait (A.S.) babu wata himma da sukakasance da itahayan sun kawar da kansu daga saran dawowar al`amarin al'umma gare su face himmar gyara musulmida tarbiyyantar da su tarbiyyarda ta dace kamar yadda Allah Ta'ala yake so daga garesu. Don haka suka kasance tare da duk wani da yake bin su kuma suka hakikanceda rashin tona asirinsu suna matukarkokarinsu wajen koya masa hukunce-lmkuncenShari'a, suna cusa masa iliminMuhammadiyya, suna sanar da shi abinda yake nasa da kumawanda yake kansa.

Ba sa daukar mutum cewa mabiyansune, daga Shi'a wansu nesai dai idanya kasance mai bin Allah, mai nesantar son zuciyarsamai riko da koyarwarsu da shiryarwarsu.

Ba su daukarcewa soyayya gare su kawai tawadatar wajen tsira, kamar yaddawasu ke gamasarda kansu daga cikin masu kageda bin sha'awace-sha'awace, kumawadanda ke neman uzurin kangarewabiyayya ga Allah su Imamai, ba sa daukarsoyayya gare su da biyayya ga shugabancinsu tsira ne saidai idan an hada da kyawawan ayyuka, an kuma yi halin biyayya gare su da gaskiya da rikon amana, da tsoron Allah da takawa.

"A'aKhaisama ka isar ga mabiyanmu cewa ba za mudauke masu komai ba dagaAllah face da aiki, kuma su ba za su samu soyayyarmu ba sai da tsoronAllah, kuma lalle mafi hasarar mutaneranar Alkiyama Shi ne wandaYa siffanta adalci sannan kuma Ya sabamasa zuwa wani abu da bashi ba."

Sai daisu suna son mabiyansu ne su kamanta masukira zuwa ga gaskiya, masu shiryarwazuwa ga alheri da rabota kuma sunaganin cewa kira a aikace yafi kira da harshe isarwa "Ku kasance masu kiranmutane zuwa ga alheri ba da harsunanku, ba. su ga kokari da gaskiya da tsoron Allah daga gare ku.

A halin yanzuza mu kawomaka wata muhawara data gudana tsakaninsu da wasu daga cikin mabiyansudomin ka san tsananin himmatuwarsu da kwadayinsu a kan gyara dabi'unmutane:

1- Muhawarar Abu Ja'afar Bakir (A.S.) shi da Jabir Ja'afi:  "Ya Jabir ashewanda yake sanya wa kansacewa shi Shi'a ne zai wadatukawai da soyayya gare mu muAhlul Bait? To wallahi babu wani Shi'amai bin mu sai dai wandaya ji tsoronAllah Ya bi shi."

Su ba a kasancean san su ba sai da kankan da kai da tsoron Allah, da amana da yawan zikirin Allah, da azumi, da salla, da bin iyaye, da alkawari ga makwabta fakirai da matalauta da mabarata da marayu tare kuma da gaskiyar magana da karatun Alkur'ani da kame harshe dagaambaton mutane sai dai da alheri, kuma sun kasance aminan jama'arsu a kan al' amura, Saboda haka kuji tsoron Allah kuma ku yiaiki saboda abinda yake ga Allah, babu wata dangantakatsakanin Allah da wani, mafi samun soyayyaa gurin Allah a cikin bayi shi ne mafificinsua tsoron Allah da kuma mafificinsu a aiki da biyayyarsa."

Ya Jabir Wallahiba mu kusantaga Allah sai dai da da'a, kuma babukubutarwa daga wuta a gare mu, kuma babu wata hujjar wania kan Allah, duk wanda ya kasancemai biyayya ga Allah to shi masoyine gare muduk wanda ya kasance mai sabo ne ga Allah to shi makiyi ne gare mu, kuma ba a samun jagorancinmu sai da aiki da tsoron Allah.

2- MuhawararAbu Ja'afar (A.S.) da Sa'idBin Hasan:1 2 next