Imam Mahadi (a.s)Marhalar karshen zamani da cin nasarar gaskiya

Rayuwar duniya tana da marhaloli mabambanta, amma abin da zamu bayar da hankali gareshi a nan ita ce marhalar karshen duniya. A wannan marhalar ce mutane da kansu zasu samu canji a ransu, su nemi rushe asasin barna tun daga asasi, a samu dawwamar hukumar gaskiya: “Allah ba ya canja abin da yake ga mutane har sai sun canja abin da yake ga kawukansu”. Ra’adi: 11. Sai Allah ya aiko musu da mataimaki daga gareshi, “... Ka sanya mana mataimaki daga gareka…”Nisa’I: 75.

A kan wannan sharadi ne Allah zai aiko da taimakonsa bisa sunnarsa ga mutanen sai barna da bata su kau, “domin bata ya kasance mai gushewa ne”. Isra’i: 81. Sai addinin musulunci ya yi galaba a kan dukkan wani addini. “… domin ya dora shi a kan addini dukkaninsa”. Saff: 9.

 A wannan marhala mutane na gari zasu gaje bayan kasa da taimakon Allah da bayyanar imam Mahadi (A.S). “Hakika duniya bayina na gari ne zasu gaje ta”. Anbiya: 105. da fadinsa: “…Mu sanya su shugabanni kuma mu sanya su masu gajewa”. Kasas: 5.

Zaman aljanna da fara halittar mutum

Sauka kasa da farkon tarihin mutum

Marhalar hadin kai  da kafa al’umma

Marhalar sabani tsakanin gaskiya da karya

Marhalar galabar gaskiya a karshen zamani

A takaice, mahangar musulunci game da wannan tafiyar tarihi ba bisa tilas ba ne. Kuma dauki ba dadi tsakanin gaskiya da karya al’amari ne na kodayaushe, da yake kama-ka-ba-ni tsakanin gyara da bata, har adalci da gaskiya su yi nasara da zuwan mai tseratar da dan Adam imam Mahadi (A.S) da taimakon Isa (A.S).

Karshen zamani a musulunci ya saba da mahangar jari-hujjar demokradiyya da kominisanci, a mahangar musulunci karshen zamani lokaci ne na cin nasara da galabar gaskiya a kan karya, daular karshen zata zama daular adalci da gaskiya da hukuma mai hukunci da addinin Allah ne, ba hukumar wurgi da addini ba, ko mai ma’unin mutum sabanin Allah. Wannan zamani zamu kawo bayanansa masu yawa da suka zo a ruwayoyin muusulunci.1 2 next