JagoranciImamanci

Mun yi imani cewa asalin Imamanci na daga cikin jiga-jigan Addini kuma imani ba ya cika sai da imani da shi kuma bai halatta a kwaikwayi iyaye a kan haka ba, ko kuma Zuriya ko masu tarbiyya kome girmansu da darajarsu kuwa, abinda yake wajibi shi ne a nemi sani a yi bincike a game da shi kamar yadda ya wajaba a yi a kan Tauhidi da Annabci.

Alal akalla imani don sauke nauyin da ke kan mukallafi baligi yana daga cikin wajiban shari'a wadanda aka wajabta masa kuma sun dogara ne a kan Imani da su tabbatarwa ko korewa koda kuwa ba jigo ba ne daga cikin jiga-jigai ba a kwaikwayon wani a kansu saboda shi kansa ta wannan bangare wajibi ne a yi imani da shi. Wato ta bangaren wajabcin sauke nauyin da ya wajaba a kansa tabbatacce daga Allah Ta' ala da kuma a hankalce, kuma ba a san su ta fuskar kwakkwaran dalili ba don haka babu makawa a koma ga wanda muka san cewa tabbas bin sa zai kai mu ga sauke nauyin da ya wajaba a kanmu, wato mu koma ga Imami ko wanda ya yi imani da Imami ko kuma wani da ba Imam ba ga wadanda suka yi imani da wanin Imam.

Haka nan mun yi imani cewa Imamanci tausasawa ne daga Allah kamar Annabci don haka babu makawa a kowane zamani ya zamanto akwai Imami mai wakiltar Annabi a aikinsa na shiryar da dan Adam, da dora su a kan abinda yake maslaha a Sa'adar duniya da Lahira, kuma biyayyar da Annabi ya cancanta daga mutane baki daya shi ma ya cancanta, domin tafi da al'amuransu da maslaharsu, da tabbatar da adalci a tsakaninsu, da gusar da zalunci da kiyayya daga tsakaninsu. A bisa wannan asasin Imamanci ya zamanto ci gaban aikin Annabci, dalilin da ke wajabta aiko da Annabawa da Manzanni ne yake wajabta ayyana Imami bayan Manzon Allah.

Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa Muke cewa: Imamanci ba ya taba yiwuwa sai da nassi daga Allah a bisa harshen Annabi ko kuma a bisa harshen Imamin da ya gabata. kuma Imamanci ba nadin ko zabin kowa ba ne a tsakanin mutane, ba al'amarinsu ba ne da idan suka so za su dasa wanda suke son dasawa ko kuma su ayyana wanda suka so ayyanawa. ya zama Imami a gare su, ko kuma a duk lokacin da suka so barin ayyanawar sai su bari su zama haka nan sakaka ba su da Imami bil hasali ma "Duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba to ya mutu ne mutuwa irin ta jahiliyya" kamar yadda haka ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a Hadisi.

A bisa wannan asasin ba zamani da daga zamuna da zai zamanta babu Imami wanda aka wajabta yi masa biyayya ba a cikinsa, wanda kuma Allah ne Ya nada shi, sawa'un mutane sun ki ko ba su ki ba, sawa'un sun taimake shi ko sun ki taimakon sa, sawa'un sun yi masa biyayya ko sun ki yi masa biyayya, sawa'un yana hallare ne ko kuwa yana suturce ne daga idandunan mutane, domin kamar yadda ya inganta Annabi (S.A.W) ya suturtu daga ganin mutane, kamar yadda ya suturtu a cikin kogo wanda game da shi Allah (S.W.T) yake cewa:

"Idan ma ba ku taimake shi ba to ai Allah  Ya riga Ya taimake yayin da wadanda suka kafirta suka fitar da shi yana na biyun su biyu yayin da suke cikin kogo yayin da yake cewa ma'abucinsa kada ka damu lalle Allah na tare da mu, sai Allah Ya saukar da natsuwarsa gare shi Ya kuma taimake shi da rundunoni da ba ku gan su ba, kuma Ya sanya kalmar wadanda suka kafirta makaskanciya kalmar Allah  kuma ita ce Madaukakiya kuma lalle Allah  Mabuwayi ne mai hikima" Surar Tauba: 40.

Ko kuma kamar yadda ya suturtu a wadi, to haka nan ya inganta Imami ya suturtu kuma babu bambanci tsakanin fakewa mai tsawo da gajera a hankalce.

Allah Ta'ala Yana cewa:

"Kuma ga kowace a'luma akwai mai shiryarwa." Surar Ra'ad: 7.1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next