Asasin SaniSani da Ijtihadi da Takalidi

Mun yi imanin cewa da yake Allah Ya Yi mana baiwar karfin tunani kuma Ya ba mu hankali to Ya umarce mu ne da mu yi nazari da tuntuntuni a kan alamun ayyukansa mu yi tunani a kan hikimarSa da kuma kyautata lura a ayoyinSa a kan duniya baki daya da kuma a kan kanmu, Allah Ta'ala Yana cewa:

"Za mu nuna musu ayoyinmu     da kuma a kawukansu har Ya bayyana gare su cewa Shi lalle gaskiya ne..." (Surar Fussilat: 53)

Kuma Ya zargi masu bin iyaye ba tambaya da cewa:

"Suka ce mu dai kawai za mu bi abinda muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba sa hankalta ne kuma ba sa shiryuwa." (Surar Bakara: 170)

Kamar kuma yadda Ya aibata masu bin zato kawai da dikake cikin duhu da cewa: "Babu abinda suke bi sai zato kawai." (Surar An'am: 116)

Alal hakika mu abinda muka yi imani da Shi Shi ne cewa: Lalle hankulanmu su ne suka wajabta mana yin tuntuntui kan halittu kamar yadda suka wajabta mana yin tunani a kan kiran wanda ya yi da'awar duk wani da Ya yi da'awar cewa shi Annabi ne da mu’uijzarsa. Kuma a gurin hankali bai dace ba a yi koyi da wani ba a cikin wadannan al'amuran kome matsayinsa da darajarsa kuwa. abinda Ya zo a cikin Alkur'ani na kwadaitarwa a kan tuntuntuni da bin ilimi da sani Ya zo ne kawai don kara tabbatar da wannan `yancin na dabi'ar halitta a hankali da suka dace da ra'ayoyin ma'abuta hankali, Ya kuma zo ne don fuskantarwa zuwa ga abinda dabi'ar hankula ta hakunta.

Bai dace ba a cikin irin wannan hali mutum ya yi wa kansa saki na dafe a kan al'amarin akida, ko kuma ya kare da dogaro a kan wadanda suka masa tarbiyya, ko kuma wasu mutane daban, lalle ma ya wajaba ne a kansa daidai yadda yake a dabi'ar karfafa kan ya yi bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi kididdiga a kan jiga jigan akidarsa wadanda ake kira jiga-jigan addini wadanda mafi muhimmancinsu su ne: Tauhidi, wato kadaita Allah, da Annabci da Imamanci da kuma Tashin kiyama.

Duk wandaYa yi koyi da iyaye haka siddan ko kuma makamantansu a imani da wadannan jiga jigan to lalle ya ketare iyaka Ya fandare daga hanya madaidaiciya kuma ba zai taba zama an yafe masa ba har abada. A takaice dai mu  muna mu muna da'awar abubuwa biyu ne:

Na Farko: Wajabcin bincike da kuma nemansani a kan jiga jigan akida bai halatta a koyi da wani ba a kansu.

Na Biyu: Wannan wajabcin wajabci ne nahankali kafin Ya zamanto na shari'a wato saninsa ba wai Ya samo asali daga nassosin addini ba ne koda yake Ya inganta su karfafa shi bayan hankali Ya tabbatar da shi.1 2 next