Akidojin Shi'a 

me ya sa muke bukatuwa zuwa ga addini?

Allah madaukaki yana cewa a ckin Alkur'ani mai girma,"ka tsaida fukarka ga addini mikakke shine halittar da Allah ya halicci mutane akanta."Rom:'30

 Abin da ake nufi da Addini shi ne wasu ilimomi da dokoki ne da Allah ya kafa ya aiko manzonsa da su domin shiryar  da a'lumma. Wadannan dokoki kuwa sun kun shi abubuwa guda uku kamar haka:

1-Akida 2-kyawawan dabi'u 3 hukunce- hukunce.Abin da muke so mu yi magana akansa anan shi ne  abin da ya shafi akida wato bangare na farko kenan. Amma kafin mu cigaba da bayani akan sa zamu fara da wasu abbuwa wato bukatuwa zuwa ga addini da kuma fa'idarsa.

Bukatuwa zuwa ga addini:

Mutum a cikn wannan duniya ba'a halicce shi ba haka nan ba tare da wata manufa ba, domin kuwa Allah mai hikima ne ba ya yin wani abu wanda babu  hikima a cikinsa. Domin idan ya kasance halittar mutum an yi ta ne ba tare da wani hadafi ba to lallai wannan zai zama kenan abu ne wanda ba bu hikima a cikinsa. Allah kuwa ba ya yin abu marar hikima don haka halittar mutum tana da manufa.

ya zo da yawa daga cikin ayoyin alkur'ani maigirma cewa Allah madaukaki ya halicci dan Adam ne domin ya samu kamala da cin nasara duniya da lahira.Saboda haka isa ga wannan hadafi kuwa yana bukatar tsari da dokoki wdanda zasu taimaka wa mutum zuwa ga wannan hadafi.Sannan kuma mutum, yana da bukatuwa zuwa ga dokoki wadan da zasu sa ya samu kwanciyar hankali da tsoro a cikin rayuwarsa ta duniya tare da 'yan'uwansa mutane.Tabbas kasancewar mutum mai takaitaccen ilimi da  tunani ba zai iya tsara wa kansa wadannan dokoki ba. Don haka mutum yana da bukatuwa zuwa ga wanda ya san matsalolinsa da abin da yake bukata, don ya tsara masa hanyar da zai bi don ya cimma  wannan hadafi nasa.Saboda haka tun da mun san cewa mutum ba wai kawai hadafin rayuwar duniya yake da shi ba, ya hada harda na gobe kiyama wato mutum yana so ne ya ci nasarar rayuwarsa duniya da  lahira, babu kuwa wanda yasan abin da zai sa mutum ya cimma wannan sai wanda ya halitta shi kuma ya san abin yake bukata, wannan kuwa ba kowa ba ne face Allah mahaliccin kowa da komi.

  Saboda haka   kamar yadda muka fada a baya cewa addini ba komai ba ne face wadannan dokoki da tsari wadan da zasu taimaka wa mutum domin cimma wannan gurin  nasa. Don haka kenan mutum yana bukatuwa zuwa ga addini.1 2 3 next