AlkiyamaTASHIN ALKIYAMA

Mun yi imani da cewa Allah zai tayar da mutane bayan mutuwarsu a wata sabuwar halitta a ranar da aka yi wa bayi alkawari game da shi. Kuma zai saka wa masu biyayya ya azabtar da masu sabo.

Wannan al'amari ne da baki dayansa da abinda ya tattara a kai dangane da abinda wanda saukakkun shari'o'i da masana Falsafa suka yi ittifaki a kai, babu wata gujewa ga musulmi ya yi ikrari da akidar Alkur'ani wadda Annabinmu mai girma ya zo da ita (S.A.W), domin wanda ya yi imani da Allah, imani tabbatacce to kuwa ya yi imani da Muhammadu (S.A.W) a matsayin Manzo daga gare shi wanda ya aiko shi da Shiriya da Addini na gaskiya haka kuma babu makawa ya yi imani da abinda Alkur'ani ya ba da labarinsa game da tashin kiyama, da sakamako da azaba, da aljanna da ni'ima, da wuta da kuma Alkur'ani ya bayyana haka a sarari kuma ya yi ishara da shi a cikin abinda ya kai kimanin aya dubu.

Idan har shakku ya shigi wani game da haka babu wani abu sai dai saboda shakkun da yake da shi game da ma'abucin sakon, ko kuma ma game da samuwar mahaliccin halittu da kudurarsa, bil hasali ma sai dai da shakkun da yake bullo masa game da asalin addinai baki dayansu, da kuma ingancin shari'o'i dungurungum.

TAYAR DA JIKKUNA

Bayan wannan, tayar da jikkuna a kebe wani al'amari ne da yake babu makawa daga cikin al'amuran Addinin Musulunci. Alkur'ani mai girma ya yi ishara gare ta:

"Shin mutum yana tsammanin ba za mu tattara kasusuwansa ba ne. E, Lalle mu masu kudurar mu daidaita yatsunsa ne."

"Idan kayi al'ajabi to abin al'ajabi ce maganarsu cewa ashe idan muka zama turbaya za a dawo da mu halitta sabuwa."

"Shin mun gajiya ne da halitta na farko a'a su dai suna cikin rudewa ne game da sabuwar halitta."

Tayar da jikkuna da ba wani abu ba ne illa sake dawo da mutum ranar tashin kiyama, ranar fitowa shi da jikinsa bayan rididdigewa da sake komar da shi zuwa ga kamarsa ta farko bayan ya zama rididdigagge.

Ba wajibi ba ne a yi imani da filla-fillan tayar da jikkuna fiye da wannan abinda akan saukinta da Alkur’ani ya yi kira game da ita a Alku’ani kuma mafi yawan ainda yake biye da ita na Hisabi da Siradi da auna aiki da aljana da wuta da sakamako da azaba duk gwarbwadon abinda bayaninsa ya zo a alkur’ani ne.

Bai wajaba ba sanin hakikancewar da babu mai kaiwa gare ta sai ma’abocin zurfin nazari mai kaifin basira kamar ilimin cewa shin jikkuna za su dawo ne da kan kansu ko kuma wasu makamantansu ne a sura? Kuma shin rayuka za su gushe ne kamar jikkuna ko kuwa za su ci gaba da kasancewa har sai sun sadu da jikkuna yayin tashin kiyama? Kuma cewa shin Tashin kiyama ya kebanta ga mutum ne ko kuwa za a hada har da dukan dabbobi ne? kuma shin komawarsu (da hukuncin Allah) tashi daya ne ko kuma sannu sannu ne? Kuma idan yin imani da Aljanna da wuta wajibi ne to ba ya zama lalle a san da samuwarsu a halin yanzu da kuma sanin cewa suna sama ne ko suna kasa ko kuma sun saba. Haka nan idan sanin ma'auni ya zama wajibi to ba wajibi ba ne a san cewa ma'aunin na ma’ana ne ko kuwa yana gurin gwada nauyi ne biyu.1 2 next