Motsa Jiki Da Shakatawa



Motsa Jiki Da Shakatawa

Samar da yanayin farin ciki da annashuwa da motsa jiki ga yara da wajen wasanni yana daga abubuwa masu muhimmanci matukar gaske, kuma daya ne daga bukatun yara masu matukar amfani. Kuma ya hau kan iyaye su karfafi ruhi da jikin yara da bayar da muhimmanci kan wannan mas'ala ta motsa jiki, annabin rahama saw a cikin maganarsa madaukakiya ya bayar da muhimmanci kan wannan mas'ala ta yara a a cikin abubuwan day a lissafa da suka hada da; koyar da littafin allah, da koyar da harbi da iyo a ruwa, da kuma barin gadon dukiya ta halal[1].

Al'ummar da take mai lafiya mai annashuwa it ace wacce take da daidaikun mutane da suke da nishadi da karfin himma, kuma ya zo a cikin dabi'un imamai (A.S) game da wasanni da motsa jiki cewa suna daga hanyoyin watayawa da karfafa ruhi da jiki wadanda suke kawo habaka da cigaba, don haka ne a fili yake cewa; muna iya gain shari'a ba ta gafala daga wannan al'amari mai muhimmanci ba.


[1] - التحفة السنية (مخطوط) – السيد عبد الله الجزائرى، صفحه: 299.