Koyon salla



Koyon salla

Mafi kyawun abin da ya faru a rayuwata ya samu asali daga garin Mash’had ne, farkon zuwanmu Mash’had sai na shiga haramin Imam Rida (A.S), saboda girman kofofin haramin sai na ce da babana shin wannan fadar sarki ce? Sai baban ya yi dariya ya ce; a’a dana fadar sarki b ace, haramin imami ne imami na sha takwas.

Bayan mun shiga haramin sai babana yayi mini bayanin dalilin da ya sa muke zuwa nan, kuma yaya yake. Yayin da na san hakan sai na tafi haramin a hankali na yi kusa da shi na jefa toman ishirin a ciki, sannan sai na roki Imam Rida (A.S) cewa ina son in iya salla saboda duk sadda na koya wajen babana na kasa koya. Amma bayan yin wannan addu’a sai na ji cewa zan iya koya.

Sai na tafi wajan littattafa da suke kusa da wurin ajiye turbobi, na zauna, na dauki wani littafin koyon salla na karanta, bayan na karanta sau daya sai na ji kamar na koya.

Sai na ce da baban: tsaya in yi salla ka saurara ko na yi daidai ko kuwa.

Ni ma na karanta da daga murya kadan. Bayan gama salla, tunda na yi alwala kuma na yi sallar azahar, sai babana ya ce Allah ya karba. Madalla ka yi daidai yaro! Sai a lokacin na ji dadi sosai.

Ali Rida Arifi mukaddam, dan shekaru 12, Tehran