AnnabciAnnabci

Mun yi imani da cewa annabci aiki ne na Allah (S.W.T) wanda shi yake daukar wadanda ya zaba daga cikin bayinsa salihai da waliyyansa kamilallu a ‘yan adamtaka ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abinda yake da amfani da maslaha gare su duniya da lahira tare da kuma da nufin tsabtace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi’u da munanan al’adu kuma da koya musu hikima  da ilimi da bayyana musu hanyoyin sa’ada da alheri domin ‘yan adamtaka ta kai kamalarta da ta dace da ita domin ta daukaka ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da na lahira.

Kuma mun yi Imani cewai Lalle ka'idar tausasawa wanda da samu za mu yi bayanin ma'anarta nan gaba ta sanya ya zama babu makawa Allah ya aiko ManzanninSa domin su shiryar da dan Adam da kuma isar da sakon gyara domin su zamanto wakilan Allah kuma halifofinSa. Kamar kuma yadda muka yi imani da cewa Allah  Ta'a1a bai dorawa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko kuma kaddamar da shi ko zabensa. Ba su da wani zabe a kan haka, sai dai al'amarin haka ga Allah  yake domin "Shi ne ya fi sanin inda zai sa sakonSa." Surar An’am Aya ta 124.

Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, kamar kumar yadda ba su da wani hukunci a kan abinda ya zo da shi na daga hukunce-hukunce da sunnoni da shari'a.

Annabci Tausasawa ne

Mutum halitta ne mai haddodi masu ban al'ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa da dabi'arsa da ruhinsa da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kan kowane daya daga cikin halayensa na dabi’a, dabi’ar son fasadi sun tattara a cikinsa kamar kuma yadda dabi’ar fizguwa zuwa ga alheri da gyara suka tattara a cikinsa, a bangare daya Allah Ta'ala yana cewa:

"Da rayi da abinda Ya daidaita ta kuma ya cusa mata fajircinta da kuma takawarta". Surar Shamsi: 7-8

"Lalle shi mutum tabbace yana cikin hasara." Surar Asri: 2.

"Lalle ne shi mutum tabbas yana dagawa. Don kawai ganin ya wadata" Surar Kalam:6-7

"Lalle zuciya tabbas mai umarni da mummuna ce". Surar Yusuf: 53.

Da sauran ayoyi makamantan wadannan da ke bayyanawa a sarari suna nuni ga irin yadda ran mutum ke kunshe da rauni da kuma sha'awa.

A bangare na biyu kuma, Ubangiji ya halitta masa hankali mai shiryarwa tare da shi wanda zai kai shi zuwa ga gyara da kuma guraren alheri da kuma zuciya mai gargadi da ke masa fada kada ya aikata mumnuna da zalunci tare da aibata shi a kan aikata abinda yake mummuna abin zargi.1 2 3 4 5 6 7 next