Yin wa’azi da shiryarwa



Yin wa’azi da shiryarwa

Yin wa’azi da nasiha da shiryarwa suna daga mafi muhimmnacin al’amuran tarbiyya ga yara, kuma iyaye suna da babbar rawar da zasu taka a nan domin shiryar da saurayi ga zabi nagari. Muna iya ganin da farko rayuwar samari da ‘yan mata cike take da matsalolin rayuwa, kuma akwai masu rashin halaye nagari domin bata su. Don haka ne ya zama wajibi kan iyaye su shiryar da su ga tafarkin kwarai da hanyar shiriya, kuma su yi amfani da tajribar rayuwa da suke da ita domin ganin sun koyar da ‘ya’yansu ita.

Su sani da yin nasiha da shiryarwa da gargadi da tsoratarwa ga Allah suna iya sanya ‘ya’yansu su tashi cikin shiriyar da ake bukata garesu da kuma al’ummarsu.

kuma ta hakan suna iya kautar da ‘ya’yansu daga fadawa tafarkin kauce hanya da barna, don haka ne ma Allah ya kawo mana misalin nasiha ta uban nan mai tausayi ga dansa a cikin Kur’ani mai girma a surar nan ta Lukman, kuma ya sanya mana wannan a matsayin kyakkyawan abin koyi ga iyaye da ‘ya’yansu[1].


[1] - اين نصايح مشفقانه را از سوره لقمان آمده است.