Yada Soyayya Ga Ahlin Gidan Annabi (S.A.W)



Yada Soyayya Ga Ahlin Gidan Annabi (S.A.W)

Tarbiyyantar da soyayyar ahlul bait as ga yara yana daga cikin mafi muhimmancin nauyin day a hau kan iyaye, da akwai hanyoyi masu yawa da na koyar da soyayya ga ahlul bait as kamar a cikin tarihinsu da koyarwarsu da zantuttukansu da ayyukansu wadanda suke masu yawa a cikin littattafai. Sannan kuma a rika sanya wa ‘ya’ya sunayen ahlul bait as da kai su wajen ziyararsu da majalisosin da ake yin a ranakun haihuwarsu ko shahadarsu, hada da kula da abincin halal ga yaro, da ambaton falalolin ahlul bait da kuma sanar da su matsayinsu as , sannan da yin salati yayin samun wani abu na farin ciki ta yadda zamu rika tunasu da yi musu salati yayin faruwar wani abu domin tunawa da su ya dawwama a kwakwalensu kuma harsunansu su nuna da ambatonsu, rayuwarsu ta cakuda da tunaninsu.

A wata ruwaya ya zo cewa: “Ku ladabtar da ‘ya’yanku a kan abubuwa uku; son annabinku , da son ahlin gidansa, da karanta kur’ani[1].

Soyayya da kauna ga ahlul bait as soyayya ce da kauna ga allah madaukaki da manzonsa (S.A.W), kuma damfaruwa ne da abubuwa masu kima na ubangiji da koyarwar addini mai girma, kuma kaiwa ga mafi daukakar matsayi ne na kamala da cikar mutumtakar dan Adam, kuma idan babu wannan soyayyar to kaiwa ga wannan kamala ba zai yiwu ba har abada, kuma idan babu ita ayyukan da mutum musulmi yake yi na alheri ba zasu karbu ba a wajen mai girma ubangijin talikai kamar yadda ya zo a wasu ruwayoyin[2]. Don haka ne ma kusanci zuwa ga Allah madaukaki da isa zuwa ga sa’adar duniya da lahira ba zai yiwu ba sai da soyayya ga annabi Muhammad da alayen Muhammad saw domin soyayyarsu an kwaba ta tare ne.


[1] - خلاصة عقبات الانوار، السيد حامد النقوى، ج 4، صفحه 255.
[2] - الهداية، الشيخ الصدوق، صفحه: 60.