Ba A Hana Yara Wasanni[1]



Ba A Hana Yara Wasanni[1]

Wasu mutane ko wasa suka ga yara suna yi to sai tsawa da zagi kamar ba a sha karantawa ba a Surar Yusuf: “Ka bar shi tare da mu a gobe, ya ji dadi, kuma ya yi wasa, kuma lalle mu masu tsaro ne gareshi”[2].. Saudayawa su yaran sukan sauwara irin wadannan mutane a kwakwalwarsu a matsayin mugwaye masu takura musu ko a matsayin makiyansu.

Don haka yana kan iyaye su saya wa yaro abin da zai rika debe masa kewa. An ce an yi wani mutum da ya hana yaransa wasa ko kadan sai yaron ya taso dolo ba kuma abin da yake so sai wasa irin na yara, da ya kai shi wajan malamai masana halin dan Adam sai suka gano ba a bar shi ya yi wasa ba ne yana yaro saboda haka suka umarci uban da ya sayo masa kayan wasa. Haka nan ya yi ta wasa har wata rana da kansa ya bar kayan wasan, da iyaye suka ce ga kayan wasanka can sai ya ce: Ai ni ba karamin yaro ba ne, ta haka ne a ka yi maganin matsalarsa.


[1] -Mukhtasaru basa’iruddarajat, Na Hasan dan Sulaiman alhilli, shafi 68. Idan ka duba zaka ga dogon labari game da nishadin imam Hasan da Husain (A.S) tun suna yara.
[2] Surar Yusuf: 12.