Wajebcin tarbiyya



Wajebcin tarbiyya

A koyarwar nan ta musulunci da Ahlul bait (A.S) sun karfafa kan tarbiyyar yaro ta zamantakewa da kuma kyawawan halaye, don haka a wannan al'umma ya kasance dole ne iyaye su kiyaye hadarin fadawa cikin miyagun halaye da sukan iya jefa yara cikin munanan halaye masu hadari, kuma wannan al'amari na tarbiyya yana farawa ne daga ranar da aka haifi yaro. Na farko dai dole ne su sanar da yaransu tahidi sahihi da yake kunshe da koyarwar kadaita allah madaukaki wacce take ba ta da wata kaucewa daga tafarki madaidaici na tsira da dora shi bisa tafarkin shiriya, da kuma kare shi daga fadawa hannun masu tunanin shaidanci da batarwa, wannan tauhidi shi ne zai kasance mataki na farko, kuma dandano mai dadi da yaro zia fara dandana kuma shuka tafarko da ya hau kan iya ye su dasa kuma su ba ta ruwa doin ta tofu ta yi karfi da kwari.

Wannan ne ma ya sanya aka yi umarnin yin kiran salla da ikama a kunnuwan yaro yayin da ya zo duniya, sai a yi kiran salla a na dama a yi ikama a na hagu, domin yaro ya fara da jin mafi dadin kalmomi kuma mafi tsarkinsu wadanda su ne tushen addini kuma asasinsa wadanda suke dauke da tauhidi da kadaita allah madaukaki, kuma su ne mafi tasiri a ruhin yaro wajen tarbiyya da dasa imani a zukatansu, kuma wannan ita ce mataki na farko da jagoran wannan duniya da lahira ya koyar da mabiyansa saw[1].

Imam sadik (A.S) ya yi nuni da cewa; shekara ta bakwai ita ce shekarar da za a fara koyawa yaro sanin tarbiyyar addini da koyar da shi hukunce-hukuncensa, yana mai cewa: ya zama wajibi ne a kan iyaye a shekara ta bakwai su sanar da 'ya'yansu haram.


[1] - الهداية، الشيخ الصدوق، صفحه: 267.