Taimakawa don yin aure



Taimakawa don yin aure

Aure wani abu ne mai daraja a cikin al’umma wanda musulunci ya shar’anta shi, kuma ya dauke shi a matsayin ibada mai girma, kuma da yin aure ne saurayi zai taka matakin farko na rabuwa da son kansa da komawa zuwa ga son waninsa ma, domin idan ya yi aure a lokacin ne zai yaye kansa daga son kansa da kebantar komai nasa da kansa domin ya sanya shi a hannun waninsa wanda yake ita ce matarsa. Kuma ta hanyar shiga wannan sabuwar marhalar ne zai cike tawayar da take tattare da shi yayin zaman gwauranci, sannan kuma ta hanyar aure ne za a kiyaye samuwar manyan gobe masu albarka, da kuma samun nutsuwar ruhi da zama waje daya, da kammaluwa da kuma biyan bukatun sha’awa ta hanyar halal, da samun lafiya cikakkiya, da amincin al’umma, da kuma biyan bukatun nan da suke damun tunanin rayinsa.

Manzon rahama mai tsira da aminci yana cewa: “Duk wanda ya yi wa ‘ya aure, kuma ya aikata gidan mijinta, to Allah zai sanya masa hular sarauta a kansa a ranar kiyama[1].


[1] - كنز العمال، المتقى الهندى، ج 16، صفحه: 451، شماره: 45383.