Tarbiyyar Yara A MusulunciTarbiyyar Yara A Musulunci

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Ka bar shi tare da mu a gobe, ya ji dadi, kuma ya yi wasa. Kuma lalle mu masu tsaro ne gareshi.[1].

Gabatarwar Mawallafi

Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannan littafi mai suna “Tarbiyyar Yara A Musulunci” domin bayani game da yadda ya kamata a tarbiyyantar da yaro, an rubuta wannan littafi ne saboda bukatar da take cikin al’ummarmu ta ganin an kiyaye hakkin yara da tarbiyyantar da su tarbiyya ta gari ta Addini wanda wannan shi ne sirrin ci gaban kowace al’umma da kuma habakarta a fagage daban-daban, kuma hanya mafi dacewa wajan ilmantarwa. Domin idan yara suka gyaru suka ta so da Azama da Kishi da Ilimi da Tunani mai kyau wannan yana nufin al’umma zata ci gaba kuma zata kai ga cimma burinta da gaggawa ba tare da wani tsoro kan haka ba.

Tun da ya kasance hadafinmu shi ne gina gida na gari da al’umma saliha wacce zata zama ta daukaka Addinin musulunci da kyawawan dabi’u a cikin al’umma shi ya sa a wannan karon muka ga ya dace mu bayar da himma wajan bincike game da yadda ya kamata a reni manyan gobe, da fatan Allah ya sa wannan aiki ya zama karbabbe a wurinsa ya kuma karfafi Addinin musulunci da shi. Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga dan’uwana Ahmad Muhammad kuma ya haskaka kabarinsa da shi.

Hafiz Muhammad Kano Nigeria

hfazah@yahoo.com

Shahribar1382 H.SH

Satumba 2003. M

Rajab 1424. H.K

Shimfida

Magana kan yara wani abu ne da babu abin da ya kai shi muhimmanci a tarihin rayuwar dan Adam Saboda su ne manya a gobe, kuma idan ba a tarbiyyatar da su yadda ya kamata ba to wannan yana nufin rushewar al’adun al’umma da shafe kufan abin da ta gada kaka da kakanni. Shi ya sa ma a tarihin juyin juya hali na kowace al’umma zaka ga yana faruwa da Yara da Samari ne sannan ya yiwu, idan mun duba tarihin Annabawa (A.S) da Manzon Rahama (S.A.W) da ma juyin da ya faru a bayansu, za mu ga ya faru ne ta hannun samari da yaran al’ummu.

Duba ka gani yadda mushirikan Makka suke cewa: Manzo ya zo ya bata tunanin samarinsu, Sabaoda samari su suke karbar canji, amma tsohon jini da ya kafu a bisa wata Akida da ta kafu a kwakwalwarsa to wannan yana da wahala ya canja sai daidaiku, don haka ne ma Ku’rani ya bayar da muhimmaci a kan shekarun samartaka zuwa arba’in.1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next