Tarihin Mace A Al'aduMace A Al’adu Da Musulunci

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Kuma idan wacce aka turbude ta da rai aka tambaye ta. Saboda wane laifi ne aka kashe ta.[1].

Gabatarwar Mawallafi

Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannan littafi mai suna “Mace A Al’adu Da Musulunci”. Wannan littafi tattararrun bayanai ne game da marhaloli da mace ta kasance a ciki daga zamanin da zuwa yau a takaice, da kuma nazarin wasu addinai game da mace.

Hadafin rubuta wannan littafin shi ne; domin mata musulmi da suke wadannan yankuna namu su fahimci irin ni’ima da Allah (S.W.T) ya yi mana ta wannan Addini da ya aiko mafificin halitta Manzo Muhammadu (S.A.W) da shi, sa’anan kuma zai taimaka musu wajan sanin matakai da marhaloli na tarihi da mata suka wuce a sauran al’ummu da ta gabata, da fatan Allah ya taimaka mana ya kuma karfafi Musulunci da shi.

Hadafin kawo irin wannan bincike shi ne fahimtar da al’umma irin ni’ima da Allah ya yi mana ta wannan Addini da yake mafi kamalar Addini a Duniya da aka aiko mafificin annabawa da shi. Abin da ya rage a kanmu shi ne gode wa Allah ta hanyar bin Addinin nasa sawu da kafa da kuma kokarin aikata duk abin da ya zo da shi ta hannun Annabinsa Muhammad (S.A.W) da wasiyyansa (A.S).

Ina rokon Allah ya bayar da ladan rubuta wannan littafi ga Iyayena kuma ya tsawaita rayuwarsu ya cika ta da sa’adar duniya da lahira.

           Hafiz Muhammad Kano Nigeria

hfazah@yahoo.com

Rabi’ul Awwl 1424 H.k

Khurdad 1382 H.SH

Mayu 2003. M1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 next