Kurkuku Bincike Da Hukunci



Kurkuku A Mahangar Musulunci (Dokokin Kasashe)

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Kuma muka yayyanka su sibdi goma sha biyu, al’ummu….[1].

GABATARWA

Ina godiya ga Allah da ya ba ni damar rubuta wannnan littafi mai suna “Kurkuku A Musulunci Da Dokokin Kasashen Duniya” A wannan karon mun yi duba ne zuwa ga ra'ayoyin Masana da Malamai da na Dokokin Kasashe da na Addinai da Mazhabobi a dunkule game da al'amarin Gidan Sarka da karfafa mana gwiwar mu rubuta shi daga Malama Fatima (Matar Marubucin) da Malam Mujtaba Adam.

Saboda ya zama mai amfani ga mutane gaba daya, da kuma kara bincike a matakin wannan zamani game da mahangar kasashe da ma wasu addinai da dokokin mafi yawancin kasashen Duniya a yau kan al'amarin Gidan Sarka da batun halarcinsa ko rashin halarcin yin sa a Musulunci ta mahangar malamai daban-daban. Koda yake muna son littafin ya zama yana da hadafi irin na littattafan da muka rubuta a baya, wato ya zama mai amfani ga al’umma da masu iko da kasashenmu ya zama sun tausaya wa talakawa da wadanda suke cikin furzin, kamar yadda ya kamata ya zama wayarwa ga na tsare ta yadda zai nemi hakkokinsa da Musulunci ko Tsarin Majalisar Dinkin Duniya ya gindaya wa Kasashen Duniya da su yi aiki da shi.

Duk da cewa ina da karancin lokaci da ya yi mini yawa amma na ga cewa yana da kyau in dan gutsuri wani lokaci domin gabatar da wannan aiki mai nauyi kuma mai amfani a daya bangaren, muna fatan Allah ya sanya shi mai amfani ga al'umma gaba daya. Duk da littafin ba shi da girma (domin ya yi saukin karantawa ga masu son bincike da karantawa) amma ya dauki kusan kwana goma wajan rubuta shi saboda karancin lokaci. Kuma kammala littafin ya zo daidai da ranan haihuwar Fatima Al-ma’asuma ‘Yar Imam Musa Al-Kazim (A.S) da kuma haihuwar daya daga Annabawa Ulul Azmi a kidayan Miladiyya Annabi Isa Dan Maryam (A.S) ranar Alhamis 25 Decemba 2003 M. daidai da 1 Zul Ka’adah 1424 H.K. daidai da 4 Di (Watan Goma) 1382 H.SH. Muna rokon Allah (S.W.T) ya mika ladan rubuta wannan littafi garesu, da kuma ga Dan’uwana Ahmad Muhammad, ya kuma haskaka kabarinsa da shi, da fatan Allah ya karbi wannan aiki namu.

Littattafan da muka rubuta zuwa yanzu, su ne: “Tarbiyyar Yara A Musulunci” da “Zabar Mace Ko Namijin Aure” da “Raddin Sukan Auren Mace Fiye Da Daya” da “Hakkoki A Musulunci” da “Mace A Musulunci Da Tarihin Al’adu Daban-daban” da “Boyayyar Taska Mai Rabo Kan Gano Ki” da “Tattaunawar Addinai Tare Da Annabi” da “Tsari Da Kayyade Iyali” da da kuma littafin da yake gabanka mai karatu.

Hafiz Muhammad Kano Nigeria

hfazah@yahoo.com

4 Di (Watan Goma) 1382 H.SH

1 ZulKa’adah 1424 H.K

25 Decemba 2003 M

 

GIDAN SARKA DOKOKI DA SANYA DOKOKI

A mafi yawan kasashe Gidan Sarka ya kara fadada da yawa, a shekarar 2000 kusan duniya tana da mutane 8.6 miliyan wadanda suke a daure ko ba a zartar da hukunci a kansu ba, kusan rabinsu sun kasance a kasar Rasha da Kasar Sin da Amerika. Kusan ‘yan sarka a Amerika sun wuce miliyan biyu wato 3.4% na yawan mutanen kasar a shekarar 1999 wato kusan yawan da yakan dadu a kowace shekara a kasar a shekara goma na karshen wannan zamani.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 next