Tattaunawar AddinaiTattaunawar Addinai (Tare Da Annabi Muhammad S.A.W)

Hafiz Muhammad Sa’id

hfaza@yahoo.com

Ka yi kira zuwa ga tafarkin ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau, kuma ka yi jayayya da su da maganar da take mafi kyau. Lalle ubangijinka shi ne mafi sani ga wanda ya bace daga hanyarsa, kuma shi ne mafi sani ga masu shiryuwa[1].

Gabatarwa

A wannan littafi mai suna “Tattaunawar Addinaiâ€‌ muna so mu yi nuni da wasu Akidu na wasu Addinai da kuma koyar da hanyar tattaunawa mafi kyau daga koyarwar Malamin Malaman Duniya kuma Mafi Ilimin dukkan bayi da Allah ya halitta, kai shi ne ma aka yi kowa dominsa wato Manzo Muhammad Dan Abdullahi Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi.

Wannan Hadisi ruwaya ce daga Sadiku Ahlul Bait (A.S) game da tattaunawar Manzo da Ma'abota wadannan Addinai wanda a cikinsa akwai hanya mai kyau ta tattaunawa da ma'abocin wata Akida da ta saba da ta mai muhawara da shi, wanda a cikinta zamu koyi tattaunawa da musayen ra’ayi ta hanya mafi kyau kamar yadda aka yi umarni a Kur’ani mai girma.

Yana kuma koyar da Hanyoyin kafa dalili na kai tsaye, da kuma Wanda ba na kai tsaye ba, da kuma hanyar bayar da jawabi da warwara mai gamsarwa, da kuma hanyar bayar da amsa da kama mutum da abin da ya yarda kuma ya yi imani da shi. A lokaci guda kuma yana iya nuna mana hakikanin manufar wadannan Addinai da yadda ma’abotansu suke fassara Akidojin addinansu. Kuma tana nuna mana yadda aka canja koyarwar Addinan da suka gabata, al'amarin da wannan al'umma ba ta tsira daga irinsa ba ta hanyar riko da Raunanan maganganu ko kuma Tafsirin da ya kafu bisa mahanga ta kuskure da yakan kai ga kurakurai wajan fahimtar Addinin Allah.

Da yake mutane a kowane zamani hali daya ne da su, al’ummar karshe ta Manzon Allah (S.A.W) ita ma ba ta fita daga irin wannan ba, shi ya sa aka samu sabani da ya kai su zuwa ga rarraba da Mazhabobi da Kungiyoyi na Akida daban-daban. Amma wani abin da za a gode wa Allah shi ne; al’ummar nan ta bambanta da sauran al’ummu domin su wadancan al’ummu bayan sun yi nesa da Wasiyyan Annabawan sukan kuma yi rashin sa’ar canza Addinin nasu gaba daya a kuma kautar da Akidunsu daga sahihancinta kamar Yahudawa da Kiristoci da Zartush da Sa’ibawa da sauransu. Amma wannan al’umma Allah ya yi alkawarin kare littafinta, shi ya sa ma duk wanda yake ganin wani yana da Kur’ani daban da wanda yake hannun musulmi to yana ganin Allah Ajizi ne daga alkawarin da ya dauka na kare littafinsa, kuma irin wadannan mutane suna a matsayin wadanda suka kafirce wa Allah ta hanyar kafircewa ayar Kur’ani mai girma.

Da yake kare littafin ya zo daidai da Ranar Shahadar Waliyyul Auliya Amirul Muminin Ali Dan Abi Dalib (A.S) wato ranan Lailatul Kadari ta biyu Lahadi 21 Ramadan 1424 H.K. Da ya zo daidai da 16 Nuwamba 2003 M. daidai da 25 Aban 1382 H.Sh. Saboda haka ne muke neman Allah madaukaki da ya bayar da ladan rubutun ga Amirul muminin (A.S) kuma ya yafe mana kurakuran ciki da tuntuben alkalami, ya sanya shi mai amfani ga al’umma kuma dalili na bincike da kara kaimi wajan neman sani.

Hafiz Muhammad Kano Nigeria

 hfazah@yahoo.com

Tattaunawar Manzon Allah (S.A.W)

Imam Sadik (A.S) ya ce: "Daga Babana Albakir (A.S) daga Kakana Ali Dan Al-Husain (A.S) daga Babansa Husain Shugaban Shahidai (A.S) daga Babansa Ali Dan Abi Dalib (A.S) cewa, wata rana ma’abota Addinai biyar suka hadu a wajan Manzon Allah (S.A.W); Yahudawa da Kiristoci da Dahariyya da Sanawiyya da Mushrikan larabawa.

 Sai Yahudawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Uzairu (A.S) dan Allah ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka shiryuwa zuwa ga gaskiya, amma idan ka saba mana zamu yi jayayya da kai. Kiristoci suka ce: Mu muna cewa Isa (A.S) dan Allah ne da ya shiga cikinsa ya hade da shi idan ka bi mu mun riga ka zuwa ga gaskiya amma idan ka saba to ma ja da kai . Dahariyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa: Halittu ba su da farko ba su da karshe suna nan har abada, kuma mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mun riga ka fahimtar gaskiya idan kuma ka saba mana to ma ja da kai. Sanawiyya suka ce: Ya Muhammad! mu muna cewa haske da duhu su ne masu juya dukkan al’amura, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu to mun riga ka fahimtar gaskiya amma idan ka saba mana ma ja da kai. Mushrikan larabawa suka ce: Ya Muhammad! Mu muna cewa: Gumaka Ubangizai ne, mun zo mu ga me kake cewa, idan ka bi mu mu mun fika mun riga ka zuwa ga gaskiya da shiriya amma idan ka saba mana to ma ja da kai.1 2 3 4 5 6 7 next