Tafarki Zuwa Gadir KhumTafarki Zuwa Gadir

Wallafar: Kamal Assayyid

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id

“Kawai Allah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa[1].

“Ni na bar muku nauyaya biyu; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayana har abada matukar kun yi riko da su[2]”

Gabatarwar Mafassari

Musulunci shi ne addinin Allah dawwamamme da yake kunshe cikin Kur’ani da Sunna, kuma Allah da manzonsa sun sani cewa al’umma zata yi sabani kamar al’ummun da suka gabace ta, don haka ne Kur’ani mai girma ya sanya wa al’umma makoma da zasu dogara da ita bayan wafatin manzo (S.A.W), wacce take haskaka musu abin da suka takaita ga fahimtarsa da tafsirinsa, wannan kuwa su ne; Ahlul Baiti (A.S).

Su tsarkaka ne daga dukkan dauda da kuma kazanta wadanda Kur’ani ya sauka ga kakansu Mustapha (S.A.W), suna karbarsa suna karanta shi suna hankaltarsa da kiyayewa, sai Allah ya ba su abin da bai ba waninsu ba, kuma manzo ya yi wasiyya da su a matsayin makoma ta gaba daya a hadisin sakalain mash’huri, wannan al’amari an gina tushensa tun ranar Gadir bisa umarnin Allah ga manzonsa da ya kafa dan amminsa imam Ali (A.S) a matsayin halifansa na farko, wanda ya sanya shi haske da wannan al’umma take shiriya da shi.

Wannan littafin yana son ya yi bincike ne game al’amarin Gadir ne kamar yadda zamu karanta cikin bayanan da shi Kamal Assayyid ya kawo, amma domin tabarruki sai ya fadada bayanin da kawo kissar Gadir kamar yadda ta zo a cikin littattafan tarihi da hadisai.

Daga karshen muna neman Allah ya gafarta mana zunubanmu domin albarkacin wannan rana mai albarka ta Gadir, ya samu cikin masu riko da wilayar imam Ali (A.S) da sauran imamai (A.S). Kuma ya bayar da ladan wannan fassara ga iyayena, ya tsawaita rayuwarsu da albarka a cikinta.1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 next