Hikimar Ziyarar KaburburaHikimar Ziyarar Kaburburan Waliyyai

Wallafar: AyatulLahi Shaikh Ja’afar Subhani

Fassarar: Yunus Muhammad Sani

Komawar: Hafiz Muhammad Sa’id

Ziyarar Kaburbura Masu Daraja

Makabarta wani wuri ne babba a cikin birni da kauye Wanda yake kunshe da matattun mutane marasa rai wanda yake dauke da babba da yaro mai iko da talaka daga magabata wadanda suke cikin barci mai zurfi da yake kamar ba za a farka ba.

 Ziyartar wannan wuri Wanda yake nuna gajiyawar dan Adam, sannan kuma yake da rawar da yake takawa wajen gusar da duk nuna iko ko kwadayin abin duniya ga mutum. Yayin da mutum mai hankali ya ga wannan wuri mai ban tsoro, zai fahimci rashin tabbatuwar duniya daga kusa, sannan ya fara tunani a kan mafita sakamkon fahimtar manufar halittar duniya da ya yi. Kuma zai sanya ya fita daga cikin magagin dimuwa da son kai, sannan ya fara tunanin neman abin zai taimaka masa wajen rayuwar da ba ta da iyaka. A kan wannan al’amari domin tarbiyyantar da al’umma Manzo (S.A.W) yana cewa: “Ku ziyarci kaburbura domin zasu tuna muku ranar karsheâ€‌[1].

Sannan a wani wurin daban yana cewa: “Ku ziyarci makabarta domin kuwa akwai darasi gareku a cikin yin hakanâ€‌.[2]

 Sannan akwai wasu daga cikin mawakan zamani kamar Marigayi Sayyid Sadik Sarmad yayin ziyarar Kasar Misra da kuma ziyarar Kaburburan fir’aunoni, sai ya yi wata a kan haka wadda take fassara hadisin manzo (S.A.W) game da hakan

Ziyartar Kaburburan Masoya1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 next